Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump na son Jordan da Masar su kwashe Falasɗinawa su koma ƙasashen da zama
- Marubuci, Alice Cuddy & Jon Donnison
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana son Masar da Jordan su ɗauki Falasɗinawa daga Gaza, wanda ya kwatanta a matsayin "wurin ragar-gaza".
Mista Trump ya ce ya tattauna ta wayar tarho da Sarkin Jordan a ƙarshen mako: "Ina son ka ɗauki mutane da dama, saboda ina kallon ɗaukacin Zirin Gaza a halin yanzu kuma wurin babu kyawun gani." Ya ce yana son neman irin wannan buƙata ga shugaban ƙasar Masar ranar Lahadi.
Matakin "zai kasance na wucin-gadi" ko kuma "na tsawon lokaci", in ji Trump.
Hamas ta sha alwashin adawa da matakin, kuma hakan zai janyo fushi da ɓacin-rai daga Falasɗinawa a Gaza, waɗanda ke ganin yankin a matsayin gidajensu na asali.
"Falasɗinawan mu a Zirin Gaza sun sha uƙuba, wasu sun mutu sanna an lalata gidaje da dama na tsawon watanni 15... ba tare da sun bar yankinsu ba. Don haka, ba za su karɓi duk wata buƙata ba, ko da kuwa buƙatar mai kyau ce wanda ke nufin sake gidna musu matsugunai, kamar yadda tayin da shugaban Amurka Trump ga Falasɗinawan ya nuna," in ji Bassem Naim, wani mamban cibiyar siyasar Hamas, a tattaunawarsa da BBC.
"Mutanen mu waɗanda suka jajirce da kuma faɗa da duk yunkurin lalata musu wurare na tsawon shekaru, za su kuma yi watsi da irin wannan buƙata," in ji shi.
An ɗaiɗaita yawancin al'ummar Gaza miliyan biyu a yaƙi da aka shafe kusan watanni 15 ana gwabzawa da Isra'ila, wanda ya janyo lalacewar muhimman gine-gine da dama a Gaza.
A baya Majalisar Ɗinkin Duniya ta kiyasta cewa an lalata kashi 50 na ababen more rayuwa a faɗin Gaza, kuma za a ɗauki gomman shekaru kafin a sake gina wuraren.
Mista Trump ya faɗi waɗannan kalamai ne yayin jawabi ga manema labarai.
"Kana magana kan mutum sama da miliyan ɗaya da rabi, kuma mun share komai," in ji shi.
"An ruguza komai a Gaza kuma mutane na ta mutuwa a can. Don haka gwara na shiga tsakani da wasu ƙasashen Larabawa da kuma gina gidaje a wurare daban-daban, wanda watakila za su zauna cikin lafiya da aminci."
Mista Trump bai yi wani ƙarin bayani kan yunkurin ba, kuma babu bayani kan haka a cikin daftarin fadar White House.
Da aka tambaye Abu Yahya Rashid, wani da aka ɗaiɗaita daga birnin Khan Younis da ke kudanci kan kalaman Trump ya ce:
"Mu za mu yanke hukunci kan makomar mu da kuma abin da muke so. Wannan yankin mu ne da kuma kakannin mu. Ba za mu tashi daga nan ba, sai dai idan gawawwakin mu ne."
Tsarin harkokin wajen Amurka na gomman shekaru ya nuna zimmar kirkiro da ƙasar Falasɗinawa, inda Gaza za ta zamanta muhimmi. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da hakan.
A baya, Amurka ta sha adawa ga duk wani yunkuri na ɗaiɗaita Falasɗinawa daga Gaza ko kuma Gaɓar Yamma da aka mamaye, inda sakataren harkokin wajen ƙasar na lokacin Antony Blinken ya faɗa a bara cewa: "Ba za a tilasta musu ba, ba za su tashi daga Gaza ba."
Sama da ƴan gudun hijirar Falasɗinawa miliyan biyu, yawanci waɗanda aka bai wa shaidar ɗan ƙasa, na rayuwa a Jordan, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya. Sun kasance ƴan uwa ga Falasɗinawa aƙalla 750,000 waɗanda suka tsere ko aka tilasta wa barin gidajensu a rikicin da ke da alaƙa da kafa Isra'ila.
Dubban Falaɗinawa ne suka tsere zuwa Masar tun bayan fara yaƙi da Isra'ila, sai dai ba a ɗaukarsu a matsayin ƴan gudun hijira a can.
A watan Oktoban 2023, shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce ya yi watsi da duk wani yunkuri na tilastawa Falasɗinawa tashi zuwa wani yanki na ƙasar, kuma mafita kaɗai ga hakan shi ne kirkiro da ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta.
Wasu daga cikin ƴan Isra'ila masu tsassaurar ra'ayi na son komawa Gaza domin gina matsugunai a can. Isra'ila ta bayar da umurnin fita daga can a 2005, inda aka ruguza matsugunai 21 sannan sojoji suka kwashe ƴan kama wuri zauna 9,000.
Tsohon ministan tsaron Isra'ila, Itamar Ben-Gvir ya ce ya yaba wa Mista Trump "saboda yunkurin mayar da mazauna Gaza zuwa Jordan da Masar."
"Ɗaya daga cikin bukatar mu wajen Firaminista Benjamin Netanyahu shi ne karfafa komawa zama wata ƙasa na dindindin," kamar yadda ya rubuta a shafin X.
Kalama Mista Trump sun zo ne a lokacin da aka jinkirta wa waɗanda aka ɗaiɗaita komawa gidajensu a arewacin Gaza bayan da Isra'ila ta zargi Hamas da take ka'idojin da aka gindaya na tsagaita wuta.
"Babu komai a can - babu rayuwa, an lalata komai. Amma duk da haka komawa yankin ka, komawa gidanka babban farin ciki ne," a cewar wani da ke cikin zumuɗin komawa gida a tattaunawa da BBC.
A wasu kalamai na daban, Mista Trump ya ce ya kawo karshen buƙatar samarwa Isra'ila da bama-bamai kusan 2,000 da tsohon shugaba Joe Biden ya amince da shi.
"Sun biya kuɗin bama-baman kuma suna jira na tsawon lokaci," kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai.
Amurka ta kasance a tsahun gaba wajen samarwa Isra'ila makamai, inda ta taimaka mata wajen kafa rundunar soji mafi kwarewa a duniya.
Sai dai yaƙin Gaza ya sake bijiro da kiraye-kiraye ga Amurka na ta rage ko kuma kawo karshen makamai da take bai wa Isra'ila, saboda irin ɓarnar da makaman suka yi a yankin.