Kano Pillars ta samu maki a Bayelsa

Asalin hoton, Getty Images
Bayelsa United ta raba maki da Kano Pillars, bayan da suka tashi 1-1 a wasan mako na biyu a gasar Premier ta Najeriya ranar Lahadi.
Pillars, wadda ake kira sai masu gida ta ci ƙwallon ta hannun Auwalu Ali Malam saura minti biyar suje hutu a wasan da suka yi a filin Samson Siasia da ke Yenegoa.
Bayan da aka koma zagaye na biyu ne tsohon ɗan wasan Tudun Wada United, Rabi'u Abdullahi, wanda ake kira Pele ya farke ƙwallon.
Da wannan sakamakon Pillars tana da maki huɗu a wasa biyu, bayan da ta fara doke Irorodu 3-0 a karawar satin farko a makon jiya.
Pillars za ta buga mako na uku a babbar gasar tamaula ta Najeriya ranar Lahadi 22 ga watan Satumba a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke jihar Kattsina.
Pillars tana buga wasanninta a Katsina, bayan da ake gyaran filinta na Sani Abacha da ke kofar mata a jihar Kano.
Ita kuwa Bayelsa za ta je Enugu Rangers, domin buga karawa ta uku ranar ta Lahadi 22 ga watan Satumba.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga ranar Lahadi:
- Tornadoes 0-0 Nasarawa Utd
- Katsina Utd 2-1 Bendel Insurance
- Akwa Utd 1-1 Abia Warriors











