Kofin Carabao: Newscastle na neman lashe kofin farko cikin shekara 56

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Lahadi mai zuwa ne za a fafata wasan ƙarshe na kofin Carabao, ƙungiyar Liverpool ke neman lashe kofin farko a ƙarƙashin jagorancin kocin Arse Slot, a gefe guda kuma ƙungiyar Newscastle ke neman lashe kofin farko a cikin shekara 56.
Liverpool ce mai riƙe da kambun, inda ta doke Chelsea a kakar bara a ƙarƙashin jagorancin Jurgen Klopp kafin ya rabu da ƙungiyar a bara.
Shekara 10 ke nan rabon wata ƙungiyar bayan Machester City da Manchester United ko Liverpool za ta lashe gasar ta EFL.
Wannan karo na biyu da Newscastle za ta buga wasan ƙarshe na kofin a ƙarƙashin jagorancin Eddie How tun bayan da wani kamfanin Saudiyya ya saye ƙungiyar. A shekara biyu da suka gabata Manchester United ta doke ƙungiyar a wasan ƙarshe.
A shekarar 1969 ce ƙungiyar Newscastle ta lashe kofi na ƙarshe, inda ta lashe kofin Inter-Cities.
"Kana shiga irin wannan wasan ne ƙarfin gwiwa da tunanin samun nasara, kuma abin da za mu yi ƙoƙarin samu ke nan," in ji Slot, wanda ƙungiyarsa ke kan gaba a gasar Premier.







