Harris ta matsawa Trump lamba kan gwajin lafiya

Kamala Harris ta bukaci abokin hamayyarta Donald Trump ya wallafa sakamakon gwajin lafiyarsa

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Adam Durbin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Kamala Harris ta wallafa gwajin lafiya da aka yi ma ta, da sakamakon ya na nuna ta na cikin koshin lafiya, kuma za ta iya zama shugabar kasa.

Bayan bayyana hakan, 'yar takarar shugabar kasa karkashin jam'iyyar Democrat mai mulki a Amurka, ta soki lamirin Donald Trump da yin kunbiya-kunbiya kan gwajin lafiyarsa.

Mataimakiyar shugabar Amurkar, ta yi ikirarin abokin hamayyar na ta, baya son mutane su san ko ya na da koshinlafiyar shugabanci ko akasin haka.

Ba tare da wallafa sakamakon gwajin lafiyarsa ba, tawagar zaben Trump ta bayyana cewa ''ya cikin koshin lafiya.''

Tawagar Trump, sun ce ayyuka sun yi wa dan takarar na jam'iyyar Replican din yawa, da kuma yakin neman zabe da suke ta fama da shi, ssun kuma yi ikirarin Harris ba ta da kamalar shugabanci idan aka kwatanta da Trump.

Wannan na zuwa ne bayan fadar White House ta wallafa cikakken sakamakon gwajin lafiyar da kwararrun likitoci suka yi wa mataimakiyar shugabar kasar, lamarin da ya fara jan hankalin Amurkawa kan lafiyar wanda zai jagorance su.

Dr Joshua Simmons, mai mukami Kanar a rundunar sojin Amurka,kuma shi ne likitan da ke kula da lafiyar Harris tsahon shekaru uku, ko a watan Afirilu ya wallafa cewa ta na kiyayewa da kula da lafiyarta yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa dangin ta su na da tarihin Kansar hanji, su na kuma fama da borin jini, amma ya ce ta na yawan bibiyar lafiyarta da kokarin shan maganin da ya dace, ciki har da gwajin kansar hanji da ta nono.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jim kadan bayan wallafa sakamakon gwajin, mai magana da yawun Haris ya wallafa a shafin sada zumunta cewa ''Saura kai Trump''.

Haka gabannin gangamin yakin neman zabe a North Carolina, Harris ta dasa ayar tambaya kan lafiyar kwakwalwar abokin hamayyarta, da ta ce ya na yawan sakin lafiya idan ya na magana.

'Yan jam'iyyar Democrat sun jima su na sukar dantakarar shugaban kasar mai shekara 78, su na magana akan cikakkiyar lafiyarsa tun daga kan lafiyar kwakwalwa, bayan jam'iyyarsa ta Republican ta dauki watanni ta na sukar lafiyar shugaba Biden, kafin ya janye daga takarar.

Idan ya yi nasara a zaben watan Nuwamba mai zuwa, Trump zai kamma wa'adin mulki karo na biyu, da kuma kasancewa mafi tsufa da ya taba zama shugaban Amurka a tarihi ya na da shekara 82 a duniya , kuma kammala wa'adin mulki.

A martanin da ya maida kan matsin lambar tawagar, daraktan yada labaran tawagar Trump Steven Cheung ya bayyana cewa bisa radin kan shi ya wallafa karin bayani game da ingancin lafiyarsa, da litan da ya ke duba shi bayyana a lokacin da ya tsallake rijiya da baya, lokacin da aka yi yunkurin hallaka shi a yakin neman zabe a Pennsylvania.

"Duk bayanan da ake bukata su na cikin sakamakon da likita ya bada a wannan lokacin, zai iya jagorantar Amurka," in ji Cheung.

Ya kuma bada misali da watan Nuwambar 2023 lokacin da Trump ya yi gwajin lafiya da sakamakon ya nuna komai lafiya, kuma garau ya ke.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna Harris na gaba da Trump da 'yar takaitacciyar tazara, amma kuma fafatawar da suke yi a gaggamin yakin neman zabe da su ke a jihohin Amurka, sun nuna ana tafiyar kunnen doki tsakanin su.

Donald Trump wurin yakin neman zabe

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Tawagar Donald Trump, ta yi watsi da zargin su na masu cewa ya na cikin koshin lafiya