Carvajal zai ci gaba da taka leda a Real Madrid zuwa 2026

Asalin hoton, Getty Images
Dani Carvajal zai ci gaba da taka leda a Real Madrid har zuwa karshen watan Yunin 2026.
Carvajal ya je Real Madrid a 2002, yana da shekara 10 da haihuwa, wanda ya fara wasa daga matasa ƴan kasa da shekara 12 har zuwa Castilla a 2010.
Tun daga kakar 2013 ya fara buga wa babbar Real Madrid tamaula, wanda yanzu yake kaka ta 12 a ƙungiyar ta Santiago Bernabeu.
Carvajal ya lashe kofi 26 a Real Madrid a wasa 427, mai Champions League shida da Club World Cup biyar da Uefa Super Cup biyar da La Liga huɗu da Copa del Rey biyu da Spanish Super Cup huɗu.
Ɗan wasan yana daga cikin biyar da suka lashe Champions League shida-shida a Real Madrid a tarihi.
Wasan karshe da Real ta doke Borussia Dortmund ta lashe Champions League na 15 jimilla a Wembley ranar 1 ga watan Yuni, Carvajal ne fitatcen ɗan wasa a karawar.
Haka kuma Carvajal zakakuri ne a tawagar Sifaniya, wanda ya buga mata wasa 50.
Ya lashe European Championship da Nations League da European Under-21 Championship da kuma European Under-19 Championship.










