Man United za ta kara da Mourinho a Europa League

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta kara da FC Porto da Rangers a gasar zakarun Turai ta Europa League da aka sauya wa fasali.
Ƙungiyar mai buga gasar Premier ta Ingila za ta fara gwabzawa da Rangers a gida kafin daga baya ta ziyarci Portugal don karawa da Porto.
Kazalika, United za ta fuskanci tsohon mai horarwarta Jose Mourinho yayin da za ta ziyarci Fenerbahce a Turkiyya.
Kowace ƙungiya za ta buga wasa takwas a zagayen farko da ake kira league phase a Turance, kamar yadda aka sauya wa babbar gasar zakarun Turai ta Champions League fasali.
An yi taron raba jadawalin ne ranar Juma'a cikin irin salon da aka yi na Champions League, amma wannan karon tsohon ɗan wasan gaba na Athletic Bilbao, Aritz Aduriz, ne ya dinga danna na'urar da ke shirya wa kowane kulob ƙungiyoyin da zai fuskanta.
Su wa Man United za ta kara da su jimilla?
A ranar Asabar za a bayyana ranaku da kuma tsarin da za a bi wajen buga wasannin gasar zakarun ta Champions League da Europa da kuma Conference League.
Manchester United
- Rangers (H)
- Porto (A)
- PAOK (H)
- Fenerbahce (A)
- Bodo/Glimt (H)
- Viktoria Plzen (A)
- FC Twente (H)
- FCSB (A)
Haka nan, Tottenham ma na cikin ƙungiyoyin da za su buga gasar ta Europa. Kulob ɗin da za ta fafata da su su ne:
Tottenham
- Roma (H)
- Rangers (A)
- AZ Alkmaar (H)
- Ferencvaros (A)
- Qarabag (H)
- Galatasaray (A)
- Elfsborg (H)
- Hoffenheim (A)
Chelsea kuma Conference League za ta buga
A ranar Alhamis ne Chelsea ta samu gurbin buga gasar ta Conference League duk da rashin nasara da ta yi a hannun Servette ta ƙasar Switzerland da ci 2-1.
Sai dai nasarar a wasan farko 2-0 da Chelsea ɗin ta yi ce ta ba ta damar cinye wasan da ci 3-2 gida da waje.
Ƙungiyoyin da Chelsea za ta buga da su:
Chelsea
- Gent (H)
- Heidenheim (A)
- Astana (A)
- Shamrock Rovers (H)
- Panathinaikos (A)
- Noah (H)












