Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Biden na fatan Amurkawa za su fahimci dalilan yi wa ɗan sa Hunter afuwan
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi wa dansa Hunter Afuwan, a manyan laifuka biyu da ya ke fuskantar barazanar dauri, duk da cewa a baya ya nuna hakan da kamar wuya.
A wata sanarwa da shugaban ya fitar, ya ce an nunawa dansa wariya a shari'ar, tare da bayyana shari'ar da mara adalci.
Hunter Biden ya amsa laifukan da ake tuhumarsa kan haraji a watan Satumba, kuma an same shi da laifin a harkar kwaya da mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba a watan Yuni - inda ya zama ɗan shugaban kasa na farko a kan mulki da aka samu da aikata laifi.
A lokacin da ya ke martani kan afuwar da gwamnati ta yi wa Hunter, Zababben shugaba, Donald Trump, ya ce afuwar da aka bai wa Hunter dafatan ta hada da na mutane shida da ake daure da su a gidan yari. Saboda suma akwai rashin adalci da bijirewa dokoki.
Trump na nufin magoya-bayansa da suka farwa ginin majalisar Capitol a ranar 6 ga watan Janairun 2021 a kokarin adawa da sakamakon zaɓen da ya kada shi a 2020.
Afuwar da Joe Biden ya yiwa ɗansa na zuwa ne bayan a baya ya nuna ba zai daga masa kafa ko sa baki a shari'ar ba.
Kuma ko a watan Satumba, Fadar gwamnati ta White House ta fito tana cewa Biden ba zai yiwa ɗan nasa afuwan ba.
Sai gashi a yammacin ranar Lahadi, shugaban ya fito yana cewa duk da ya yarda da tsarin shari'ar kasar, siyasa ta shiga batun don hakan akwai rashin adalci a shari'ar.
Biden da ke nuna cewa wannan yanayi da matakin da ya dauka abu ne mai wahala a gareshi ya na fatan Amurkawa za su fahimci matsayinsa na Uba da kuma shugaban kasa a irin wannan lokaci.
A wata sanarwa da shi ma da ya fitar, Hunter Biden ya ce kura-kuran da ya aikata sun kasance abin da aka tattara wajen samun hanyar cin mutunci da tozarta danginsa saboda buri na siyasa.
Hunter Mai shekara 54 a duniya ya shafe shekaru 5 da rabi yana bakin ciki da zub da hawaye a cewar mahaifinsa.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da shugaban Amurka ke irin wannan afuwa ga jininsa ba.
Bill Clinton shi ma ya taba irin wannan afuwa ga kaninsa, Roger Clinton kan laifukan da suka danganci ta'ammali da hodar Iblis da aka zargeshi da aikatawa a 1985, amma ya yafe masa a 2001.
Sannan a 2020, Donald Trimp shi ma ya yafewa Charles Kushner, sirikin diyarsa Ivanka.
Kuma ko a wannan lokaci Kushner na cikin mutanen da Trump ya bai wa mukami a sabuwar gwamnatinsa.