Raphinha ne gwarzon La Liga na Agusta

Asalin hoton, Getty Images
Raphinha ne aka zaɓa gwarzon La Liga na Agusta, bayan da Barcelona ta lashe wasa huɗu da fara kakar bana.
Ɗan kasar Brazil ya ci ƙwallo uku a watan Agusta da bayar da biyu aka zura a raga, inda ƙungiyar Sifaniya ta yi nasara a dukkan karawa huɗu,
Ya taka rawar gani a wasan farko da Barcelona ta je ta ci Valencia 2-1 da wanda ta doke Athletic Club, sai ya bai wa Pedri ƙwallon da ya zura a ragar Rayo Valecano da Barcelona ta yi nasara 2-1.
Wasan da ya fi sa ƙwazo shi ne wanda Barcelona ta caskara Real Valladolid 7-0, wanda ya ci ƙwallo uku rigis da bayar da ɗaya aka zura a raga.
Wannan shi ne karon farko da Raphinha ya lashe ƙyautar a bana, kuma ta farko tun bayan da ya koma Sifaniya da taka leda.
Haka kuma Hansi Flick na Barcelona shi ne ya lashe ƙyautar fitatcen koci a watan Agusta a La Liga, bayan jan ragamar lashe karawa huɗu da fara kakar nan.
Sannan Lamine Yamal, shi ne ya lashe ƙyautar matashin ɗan wasa da ba kamarsa a watan Agusta a La Liga.
Ranar Lahadi 15 ga watan Satumba ne Girona za ta karɓi bakuncin Barcelona a wasan hamayya na mako na biyar a La Liga.










