Makomar: Musiala, Toney, Varane, Amorim, Gallagher, Patino

An wallafa

Manchester City na sahun gaba a neman dauko dan wasan gaba na Jamus mai taka leda a Bayern Munich Jamal Musiala mai shekara 21, amma kungiyoyin Liverpool, Barcelona da Paris St-Germain su ma na son dan wasan. (Independent)

Brentford na fatan dan wasan gaban Ingila Ivan Toney zai bar kungiyar a karshen kakar wasa, sai dai Bees za su bukaci fam miliyan 50 kan kan dan wasan, inda Manchester United ke cikin kungiyoyin Premier League da ke zawarcin dan wasan mai shekara .28 (HITC)

Sir Jim Ratcliffena na tattaunawar keke-da-keke da dayan mai kungiyar Newcastle United Amanda Staveley a kokarin cimma yunkurin cimma matsaya kan komawar daraktan sporting Dan Ashworth komawa Manchester United. (Times - subscription required)

Kwazon da dan wasan gaba na Jamus da ke taka leda a Arsenal ya nuna, ya sanya Gunners sun fara tunanin shirin musayar dan wasan Kai Havertz, mai shekara 24, sai dai babu tabbas kan makomar sa Toney.(Mirror)

Ba za a sake baiwa dan Faransa Raphael Varane, mai shekara 30, bai shiga sabon kwantiragi ba, kan ainahin kudin da Manchester United ta taya, kuma ana sa ran zai bar kungiyar da zarar kwantiragin shi ya kare a watan Yuni mai zuwa. (Chris Wheeler, Mail)

Dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Arsenal Charlie Patino mai shekara 20, ya shirya tsaf domin musayar shi a kakar wasa mai zuwa.(Evening Standard)

Liverpool ta amince da tsarin shugaban Sporting Lisbon Ruben Amorim. (Football Insider)

Manajan kungiyar Tottenham Ange Postecoglou, ya samo sabon dan wasan tsakiya a daya daga cikin sayo 'yan wasa masu muhimmanci, an kuma sanya dan wasan Bayer Leverkusen, kuma dan Ecuador Piero Hincapie, mai shekara 22, a cikin jerin 'yan wasan da ya ke nema. (Bild, via TeamTalk)

Spurs na son dauko dan wasan Algeria kuma mai taka leda a Union Saint-Gilloise Mohamed Amoura a kakar wasannan, sai dai kuma ita ma kungiyar West Ham da Wolves na zawarcin dan wasan mai shekara 23. (GiveMeSport)

Shugaban Newcastle ya zuba fam miliyan 37 a matsayin sabon jari a kungiyar, duk da ba a bayyana ko za a yi amfani da kudin idan an bude kasuwar saye da saida 'yan wasa ba. (Football Insider)