Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta ɗauki Adarabioyo daga Fulham
Chelsea ta ɗauki ɗan wasan baya na Fulham Tosin Adarabioyo kyauta bisa yarjejeniyar shekara huɗu.
Adarabioyo mai shekara 26 zai koma Stamford Bridge ne idan kwantaraginsa ya ƙare a ƙarshen watan nan, kuma an fahimci cewa yana so ya koma can ne don ya buga gasar zakarun Turai ta Europa Conference League.
Tsohon ɗalibi a Manchester City, Adarabioyo ya ƙi amincewa da sabon tayin da Fulham ta yi masa a watan Afrilu, inda zai zama ɗan wasan mafi yawan albashi a ƙungiyar.
"Chelsea babban kulob ne kuma wannan lokaci ne mai muhimmanci a gare ni. An haife ni mil uku kacal daga Stamford Bridge kuma a nan na fara buga ƙwallon ƙwararru," in ji Adarabioyo.
"Ina cikin farin ciki sosai kuma na ƙagu na fara taimaka wa kulob ɗin cimma abin da muka sa a gaba."
Chelsea na fatan zuwan ɗan wasan zai taimaka wajen hanzarta tafiyar Trevoh Chalobah, wanda Man United ke nema.
Thiago Silva mai shekara 39 ma zai bar Chelsea zuwa Fluminense ta Brazil kafin sabuwar kaka.