Barcelona ta shiga jerin waɗanda Bellingham ya zura wa kwallaye

An wallafa

Barcelona ta yi rrashin nasara a gida a hannun Real Madrid a wasan mako na 11 a gasar La Liga karawar El Clasico ranar Asabar.

Minti shida da take leda Barcelona ta ci kwallo ta hannun tsohon ɗan wasan Manchester City, Ilkay Gundogan, haka suka je hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Real ta farke ɗaya ta hannun Jude Bellingham, sannan ya kara na biyu daf da za a tashi wasan.

Ɗan wasan Ingila ya ci kwallo 10 a bana a La Liga da uku a Champions League, ya zura ɗaya a ragar Scotland a wasan sada zumunta da Ingila ta yi nasara 3-1.

Da wannan sakamakon Real Madrid, wadda ta yi wasa 11 tana ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 28, sai Girona ta biyu mai maki iri ɗaya da na Real.

Barcelona tana ta uku da maki 24, yayin da Atletico Madrid wadda za ta karɓi bakuncin Deportivo Alaves ranar Lahadi ke ta huɗu da maki 22, bayan wasa tara.

Ranar Lahadi 5 ga watan Nuwamba Real Madrid za ta karɓi bakuncin Rayo Vallecano, ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Sociedad ranar Asabar.