Bayanan da BBC ta tattara kan ƴan Gaza da suka mutu lokacin raba kayan agaji

An wallafa

Aƙalla Falasdinawa 112 aka kashe yayin da jama’a suka yi yi wa manyan motocin dakon kayan abinci ƙawanya da safiyar ranar Alhamis, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Hamas ta sanar.

Ɗaruruwan mutane ne suka yi dirar mikiya a jerin gwanon matoci lokacin da suke kan hanya zuwa Arewaci cikin duhu a wajen birnin Gaza, tare da rakiyar sojojin Isra'ila.

Ƙari kan adadin waɗanda suka rasa rayukansu, akwai kuma wasu 760 da suka samu muggan raunuka in ji ma'aikatar.

Ibtila'in ya haifar da ce-ce-ku-ce game da abin da ya faru da kuma waɗanda suke da alhakin kashe rayuka.

Sashen Gano Gaskiya na BBC ya dubi bayanai masu muhimmanci game da al'amarin, tushe da kuma lokacin da abin ya faru. Mun duba bidiyo a shafukan sada zumunta da bayanan da na'urori suka ɗauka da kuma hotunan da aka ɗauka ta hanyar amfani da jirgi maras matuki, mun tattara su guri ɗaya don bayyana abubuwan da muka sani da waɗanda ba mu sani ba game da abin da ya faru zuwa yanzu.

Ɗaruruwa na jiran agaji

An wallafa bidiyon a Instagram da ƙarfe 23:30 na ƙasar a ranar 28 ga watan Fabarairu, yana ɗauke da yadda ɗaruruwan mutane suke kewaye wuta yayin jiran kayan agajin.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin ɓarkewar yunwa a Arewacin Gaza, inda kimanin mutum dubu ɗari uku ke rayuwa cikin ƙarancin abinci da rashin tsaftataccen ruwan sha, yankin ya fuskanci ƙarancin kayan agaji a makonnin nan.

Bidiyon ya nuna cunkoson mutane a titin al-Rashid a yankin Kudu maso Yammacin birnin Gaza. Shi ne kuma gurin da aka yi amfani da shi a baya-bayan nan a matsayin cibiyar rabon kayan agaji.

A baya mun tantance bidiyo da shaidu daga yanki waɗanda suka yi mana bayanin ƴan Gazan da aka kashe a cibiyar saukar da kayan agajin.

Mahmoud Awadeyah, ɗan jarida ne da ya kasance a yankin, ya shaida wa BBC cewar: "Akwai mutane da dama da suke neman abin da za su ci da kuma buhun garin alkama."

Ayarin motocin sun tunkari sansani

Da karfe 04:00 agogon ƙasar a ranar Alhamis 29 ga watan Fabrairu, ayarin motocin dakon kaya da ke ɗauke da kayan agaji daga ƙasar Masar sun bi ta wani yanki da dakarun tsaron Isra'ila (IDF) suke, daga nan suka nufi Arewa hanyar titin al-Rashid.

Rundunar ta IDF ta ce akwai manyan motocin dakon kaya 30 a cikin ayarin, yayin da wani da ya shaida lamarin ya faɗa wa BBC cewar motoci 18 ne ko - ƙasa da haka.

Babban mai magana da yawun rundunar tsaron Israila IDF, Daniel Hagari ya ce da karfe 04:45 mutane suka yi wa motocin dakon kaya ƙawanya, lokacin da motocin suke tunkarar shataletalen Nabulsi, da ke Kudu maso Yammacin birnin Gaza.

Muntane sun yi wa motocin dakon kaya ƙawanya

Bidiyon da rundunar tsaron Isra'ila ta fitar yana da yawa, an yi masa gyara zuwa sassan huɗu.

Ya nuna faruwar al'amarin a wurare biyu, kuma duk BBC ta tantance yankunan.

Ɓangarori biyu na bidiyon sun nuna yadda mutane suka kewaye motoci biyu ko fiye a Kudancin shataletalen Nabulsi.

Abubuwan da suka faru ga jerin gwanon motocin dakon

Sauran sassa biyu na bidiyon sun nuna abubuwan da suka faru kusan mita 500 daga Kudu.

Sun nuna aƙalla manyan motocin haya guda huɗu. Kuma ana iya ganin mutane suna ta kewayawa a kusa da su, amma a wannan karon ana iya ganin kamar wasu abubuwa marasa motsi ne kwance a ƙasa.

Hoton bidiyon na rundunar tsaron Isra'ila da aka haska da jar kala.

Har ila yau, ya nuna motocin sojojin Isra'ila a kusa.

Sashen Gano Gaskiya na BBC ya nemi rundunar tsaron Isra'ila ta ba shi cikakken hoton abin da ya faru.

Harbin bindiga

Mun bincika bidiyon musamman na Al Jazeera da aka ɗauka kusa da yanki na biyu a bayan ayarin, kusan rabin kilomita Kudu da shataletalen.

Ana iya jin ƙarar harbe-harbe kuma ana ganin jama'a na cincirindo kan manyan motocin ɗaukar kaya. Kuma ana iya ganin fitilun tsaro na haska sararin sama.

Mahmoud Awadeyah ya ce motocin Isra'ila sun fara harbin mutane lokacin da agajin ya isa.

"Da gangan Isra'ila ta harbe mutanen, yayin da suke ƙoƙarin zuwa kusa da motocin dakon garin alkama.''

"Kai tsaye aka harbe su kuma aka hana mutane zuwa kusa da waɗanda aka kashe.''

Bayan faruwar al'amarin

Mun tabbatar da wasu hotunan bidiyo da aka ɗauka inda aka yi harbe-harben gawarwakin da aka zuba cikin wata motar ɗaukan kaya wadda ke hanyar zuwa Arewacin shataletalen Nabulsi.

An samu rahotannin cewa an kai waɗanda suka jikkata asibitoci da dama.

Dr Mohamed Salha, babban jami'in asibitin wucin gadi ne na al-Awda, inda aka kai da dama daga cikin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata, ya shaida wa BBC cewa: “Asibitin Al-Awda ya karɓi kusan mutane 176 da suka jikkata, yayin da 142 daga ciki suke ɗauke da raunukan harsashi, saura kuma sun samu rauni ne sakamakon turmutsutsu.''

Martanin Isra'ila