Isra’ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar kai agaji Gaza

An wallafa

Isra’ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar bari a shiga da karin kayayyakin agaji Zirin Gaza wanda yaki da lalata, kamar yadda masu shiga tsakani na Qatar suka bayyana.

Sun ce a karkashin yarjejeniyar wadda Qatar din da Faransa suka jagoranta, za a bayar da magani ga ‘yan Isra’ila da Hamas ta yi garkuwa da su.

Ita kuwa Isra’ila za ta bari a shigar da muhimman kayayyakin da ake matukar bukata a Gaza.

Bangarorin biyu da ke yaki da juna, Hamas da Isra'ila, sun cimma wannan muhimmiyar yarjejeniya ne da ake ta faman ganin an same ta bayan da yanayi ya tsananta a Gaza, bayan sama da wata uku na ruwan bama-bamai da Isra’ila ke yi wa yankin.

Bayan wannan Amurka, da ke zaman babbar kawa ga Isra’ila, ta ce tana da kwarin gwiwar cewa za a saki karin ‘yan Isra’ila da Hamas ta yi garkuwa da su.

Jakadan Amurka na musamman a Gabas ta Tsakiya ya kasance a Qatar domin tattauna yuwuwar wannan yarjejeniya ta sakin mutanen , kamar yadda kakakin fadar gwamnatin Amurka a kan tsaro John Kirby ya sanar a jiya Talata, inda ya ce an bai wa tattaunawar muhimmanci sosai, kuma suna da fatan cewa za ta cimma nasara ba da jimawa ba.

Kafin nan an jiyo kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar, Majed Al Ansari yana bayar da sanarwar cimma yarjejeniyar kai kayan agajin.

A bisa yarjejeniyar kayan za su bar babban birnin Qatar din Doha, zuwa Masar a ranar Laraba.

Daga can kuma sai a nufi Gaza da su, inda za a raba su ga fararen hula yayin da magungunan kuma za a mika su ga ‘yan Isra’ila da Hamas ta yi garkuwa da su.

Sama da Yahudawa 132 ne aka yi amanna har yanzu suna rike a hannun Hamas a Gaza.

Kusan mutun 240 ne mayakan Hamas suka kama tare da garkuwa da su a wasu jerin hare-hare na ba-zata da suka kai kudancin Isra’ila ranar bakwai ga watan Oktoba na 2023.

A farmakin sun kuma kashe mutum aƙalla 1200, yawanci farar hula, kuma wannan ne ya bude kofar yakin da hamas din ta kaddamar a kan Gaza wanda a yanzu ya shiga wata na uku.

A wata wasika da kungiyar iyalai da ‘yan uwan wadanda aka yi garkuwa da su ta aika ga majalisar yaki ta Isra’ila, bayan da yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta kare a shekarar da ta wuce, kungiyar ta ce wasu daga cikin mutanen na bukatar kula da lafiyarsu akai-akai wasu ma kuma na cikin hadari.

A makon da ya gabata, Firaministan Isra’ilar Benjamin Netanyahu ya ce shugaban hukumar leken asiri ta kasar, Mossad, David Barnea, ya tuntubi Qatar domin sihiga tsakani a yi yarjejeniyar samar da magungunan.

A ranar Talata Netanyahun ya fitar da wata sanarwa da a ciki yake yabo da godiya ga dukkanin wadanda suka taimaka wajen yin yarjejeniyar.

Zuwa yanzu dai a hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza ta kashe Falasdinawa sama da 24,000 yawancinsu mata da kananan yara, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza.

Haka kuma hukumomin Falasdinawa sun ce kashi 85 na al’ummar Gaza sun rabu da muhallinsu a sanadiyyar ruwan bama-bamai na Isra’ila.

Ana ci gaba da matsa wa Isra’ila lamba kan ta dakatar da hare-haren saboda mummuna halin da fararen hula ke ciki a Gaza.

Hatta babbar kawarta, Amurka ma wadda ke kare ta a kan yakin, ta yi ta gaya wa Firaminista Netanyahu cewa yawan farar hula da hare-haren ke hallakawa ya yi yawa sosai.