Al-Hilal za ta sanar da daukar Messi, Ancelotti zai dauko Kane

Asalin hoton, Reuters
Manaja Carlo Ancelotti ya fadawa shugabannin Real Madrid cewa ya na son dauko dan wasan Tottenham da kuma Ingila Harry Kane, mai shekara 29. (The Athletic)
Kungiyar Al-Hilal ta Saudi ta na sa ran sanarda daukar dan wasan gaba na Paris St-Germain da kuma Argentina Lionel Messi, mai shekara 35, ranar 6 ga watan Yuni. (SPORT)
Chelsea ta na da kwarin gwiwa za ta dauki dan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte mai shekara 22 daga kungiyar Sporting Lisbon. (Fabrizio Romano)
Paris St-Germain ta na hangen dauko dan wasa mai tsaron gida na Arsenal Gabriel Magalhaes mai shekara 25. (Goal)
Liverpool ta na zawarcin dan wasan Fulham da kuma Netherlands Kenny Tete, mai shekara 27. (Sun)
Dan wasan tsakiya na Brighton da Argentina Alexis Mac Allister mai shekara 24 ya shirya komawa Liverpool. (Fabrizio Romano)
Mai tsaron raga na Tottenham da Faransa Hugo Lloris mai shekara 36, ya yi ritaya daga taka leda. (Nice Matin - via Evening Standard)
Leeds United ta lissafa shugaban Blackburn Rovers Jon Dahl Tomasson cikin wadanda ta ke zawarci su zama manajanta (Football Insider)
Shugaban Chelsea Mauricio Pochettino zai dakile duk wani yunkurin Real Madrid na sayan Kai Havertz mai shekara 23. (AS - via Metro)











