Valverde ya buga wa Real Madrid wasa na 300

Fede Valverde

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta doke Atletico Madrid 2-1 a wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League da suka kara ranar Talata.

Fede Valverde ya buga wasan a Santiago Bernabeu karo na 300 da ya yi wa Real Madrid jimilla a gasa shida.

Ɗan kasar Uruguay ya fara yi wa Real Madrid wasa ranar 23 ga watan Oktoban 2018, an kuma ci wasa 203 da shi a fili, ya zura ƙwallo 29 a raga.

Haka kuma ɗan wasan ya lashe kofi 14 a Real Madrid, kakar da ya buga wasa da yawa a Real ita ce a 2022/23, wanda ya buga karawa 56.

Real da Atletico sun kara karo uku a kakar nan da wasa biyu a La Liga gida da waje da suka tashi 1-1 kowanne.

Sai dai Real ta yi nasara 2-1 a kan Atletico a Champions League, Atletico za ta karɓi bakuncin karawa ta biyu ranar Laraba 12 ga watan Maris.

Atletico ce ta biyu a teburin La Liga, yayin da Real Madrid ce ta uku.

Jerin wasa 300 da Valverde ya buga tsakanin gasa shida:

La Liga 199

Champions League 63

Copa del Rey 22

Spanish Super Cup 11

Club World Cup 3

European Super Cup