Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real ta yi atisayen tunkarar Alaves a La Liga ranar Lahadi
Real Madrid ta yi atisayen tunkarar wasan mako na 31 a La Liga da za ta je Mendizorroza, domin karawa da Deportivo Alaves ranar Lahadi.
Ƴan wasan Real Madrid sun fara da motsa jiki da guje-guje, sannan kowa ya yi wasa da tamaula yadda ya kamata.
Daga nan aka raba filin biyu, inda aka dunga bani in baka, sai kuma aka koma da gwada masu tsaron raga.
Har yanzu Alaba da Mendy da Lunin sun yi atisaye su kaɗai ba a cikin ƴan wasa ba.
Real ta doke Alaves 3-2 a wasan farko a kakar bana a La Liga ranar Talata 24 ga watan Satumbar 2024.
Ƙungiyar Santiago Bernabeu tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 63 da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama.
Ita kuwa Alaves tana ta 17 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Sifanuta da maki 30, bayan karawar mako na 30.
Real Madrid za ta buga wasan na La Liga ranar Lahadi, domin shirin karɓar bakuncin Arsenal a wasan Champions League ranar Laraba, zagayen kwata fainal.
A makon jiya ne Arsenal ta doke Real 3-0 a wasan farko karawar daf da na kusa da karshe a Emirates a babbar gasar zakarun Turai.