Portugal za ta kara da Morocco a Quarter Finals a Qatar

Portugal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Portugal ta caskara Switzerland da ci 6-1 a wasan zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya da suka buga ranar Talata a Qatar.

Minti bakwai da fara wasa Goncalo Ramos ya fara cin kwallo a karon farko da Porugal ta saka shi a wasa a kuma gurbin Cristiano Ronaldo.

Haka shi ne ya kara biyu wato uku rigis ya ci a karawar - ya zama na farko da ya ci kwallo uku a wasan farko a kofin duniya, bayan Miraslove Klose na Jamus a 2002.

Sauran da suka ci kwallayen sun hada da Kepler Laveran Pepe da Raphael Guerreiro da kuma Rafael Leao.

Switzerland ta zare daya ta hannun Manuel Akanji a minti na 58.

Da wannan sakamakon Portugal za ta fuskanci Morocco a wasan Quarter finals ranar Asabar 10 ga watan Disamba.

Morocco ta kai daf da na kusa da na karshe, bayan nasara a kan Sifaniya da ci 3-0 a bugun fenariti.

Sai daga baya aka sa Cristiano Ronaldo a wasan - a karon farko da ya yi zaman benci a manyan wasan Portugal tun 2008.

A lokacin a kuma fafatawa da Switzerland kenan yanzu wasa 31 ne tsakanin.