Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah na fuskantar tangarɗa

    • Marubuci, Jaroslav Lukiv & David Gritten
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hare-haren Isra'ila ta sama a Lebanon da harba bama-bamai da Hezbollah ta yi a Isra'ila sun sa an fara fargabar za a samu tsaikon yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon.

An kashe mutum 10 a kudancin Lebanon a daren Litinin, kamar yadda ma'aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana, bayan Isra'ila ta kai wasu hare-hare da suka fi zafi tun bayan da ɓangarorin biyu suka amince da tsagaita wuta.

Sojojin Isra'ila sun ce mayaƙan Hezbollah suka kai wa harin, sannan suka buƙaci hukumomin ƙasar Lebanon da su hana abin da suka kira, "aikace-aikacen" ƙungiyar.

Hezbollah ta harba bama-bamai biyu a sansanin sojin ƙasan Isra'ila, inda ta ce hare-haren gargaɗi ne saboda abin da ta kira "yi wa yarjejeniyar da aka shiga karan-tsaye" daga ɓangaren Isra'ila. Sai dai ba a samu rahoton rasa rai ba.

Amurka, wadda tare da taimakon Faransa ta shiga tsakani wajen ƙulla yarjejeniyar, ce take bibiyar yadda ake amfani da ita, sannan ta ce ana amfani da yarjejeniyar (sosai) duk da matsalolin da ake samu.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, an ba Hezbollah kwana 60 ta janye sojojinta a bakin iyakar Lebanon da Isra'ila da kuma yankin tekun Lithani, kimanin tafiyar kilomita 30 (mil 20) ta arewaci.

Sojojin Isra'ila suma za su janye daga yankin, sannan a maye gurbinsu da sojojin Lebanon da sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.

An fara yaƙin ne a ranar 8 ga Oktoban 2023 lokacin da Hezbollah ta harba wasu rokoki a arewacin Isra'ila domin goyon bayan mutanen yankin Falasɗinu a Gaza bayan Hamas ta kai wani mummunan hari a kudancin Isra'ila.

Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama masu tsanani, sannan ta kutsa ta ƙasa a ƙarshen watan Satumba, inda ta ce tana so ta tabbatar ƴan ƙasarta 60,000 da hare-haren rokokin Hezbollah suka raba da muhallansu a arewacin ƙasar sun koma gidajensu.

Hukumomin ƙasar Lebanon sun ce sama da mutum 3,960 ne aka kashe a yaƙin, ciki har da fararen hula masu yawa, sannan kusan mutum miliyan 1 ne aka raba da muhallansu.

Suma hukumomin Isra'ila sun ce an kashe sojojin Isra'ila sama da 80, da fararen hula 47.

Kamfanin dillancin labarai na gwwamnatin Lebanon, NNA, ya ruwaito cewa jiragen saman Isra'ila sun kai hare-hare aƙalla guda 11 a kudancin Lebanon a daren Litinin.

Daga cikin wuraren da suka kai harin akwai birnin Haris, inda ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce an kashe mutum shida, sannan biyu suka jikkata.

An kashe wasu mutum huɗu, sannan aka jikkata wani mutum ɗaya a birnin Tallousseh, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.

Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana a wata sanarwa cewa, "ta kai hari a kan ƴanta'addan Hezbollah, da gomman makamai da kadarorinsu a Lebanon."

Ta kuma ce ta kai hare-hare a inda Hezbollah ke amfani da shi wajen harba bama-bamai zuwa yankin Mount Dov/Shebaa da ke tuddan Golan.

"Harba bama-bamai da Hezbollah ta yi ya saba ƙa'idar yarjejeniyar da aka shiga tsakanin Isra'ila da Lebanon."

"Isra'ila ta kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a Lebanon su cika nasu ɓangaren yarjejeniyar, kuma su hana Hezbollah daga taruwa a cikin yankunan ƙasar."

Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce, "a shirye yake ya cigaba da amfani da yarjejeniyar, amma zai mayar da martani a duk lokacin da Hezbollah ta saɓa yarjejeniyar - ƙarami ko babba."

Hezbollah ta tabbatar da cewa ta harba bama-bamai a Isra'ila, inda ta ce gargaɗi ne a kan, "yadda sojojin Isra'ila suke saɓa yarjejeniyar da aka shiga."

Tun da farko a ranar Litinin, hukumomi a ƙasar Lebanon sun ce hare-haren Isra'ila sun kashe mutum biyu a kudancin ƙasar.

Ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce an kashe mutum ɗaya a Marjaoun, sannan hukumar leƙen asirin Lebanon ta ce harin jirgi mara matuƙi ya kashe wani jami'inta a Nabatieh.

Rundunar sojin Lebanon ta ce an jikkata wani soja da yake aikin sintiri lokacin da wani jirgi mara matuƙi ya kai hari a birnin Hermel da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta "ta kai hare-hare ne a kudancin Lebanon domin wasu ayyukan Hezbollah a yankin, waɗanda suke barazana ga fararen hula na Isra'ila, wanda hakan ya saɓa yarjejeniyar da aka shiga ne."

"Mun samu labarin wani sojan Lebanon da aka jikkata a hare-haren, amma muna bincike."

Shugabana majalisar Lebanon, Nabih Berri, wanda yake tausayin Hezbollah, wanda kuma ya kasance cikin waɗanda suka shige gaba wajen tsara yarjejeniyar, ya ce, "hare-haren da Isra'ila ta yi ya saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka shiga."

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noël Barrot ya faɗa wa takwaransa na Isra'ila, Gideon Saar, ta wayar tarho cewa akwai buƙatar, "kowane ɓangare ya girmama yarjejeniyar."

Sai dai a wani faifan bidiyo da ake yaɗawa a kafofin sadarwa, Saar, ya ce, "mun ji an ce Isra'ila na saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta, alhalin ba haka ba ne, ɗaya ɓangaren ne ke karya alƙawarin."

Ya yi gargaɗin cewa Isra'ila za ta cigaba da ɗaukar mataki a duk lokacin da aka hango Hezbollah a kudancin tekun Lithani ko suka yi yunkurin kai makamai yankin.

"Zan ƙara faɗa da babbar murya - Isra'ila na girmama yarjejeniyar da aka shiga ta tsagaita wuta, amma ba za mu amince a koma gidan jiya ba."

Hukumomin ƙasar Amurka sun bayyana cewa yarjejeniyar tana samu nasara, amma akwai "sauran aiki a gaba."

"Maimakon gomman hare-haren da Isra'ila ke yi, yanzu an koma ɗaya ko biyu a rana," in ji kakakin hukumar tsaron Amurka, John Kirby a zantawarsa da manema labarai. "Za mu cigaba da ƙoƙari domin ganin an daina hare-haren baki ɗaya."