Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Halin da aka shiga a Gaza ranar da aka katse hanyoyin sadarwa
Wani ɗan jarida ya aiko da saƙon murya a Gaza, inda aka katse hanyoyin sadarwa.
A cikin tsakiyar saƙon, an ji ƙarar fashewar bam.
"Yanayin na da ban tsoro, "in ji shi, yana mai cewa mutane da dama ba su san makomar ƴan uwansu ba.
Saƙon na WhatsApp da aka aiko daga birnin Deir al-Balah a ranar Asabar, ya bayar da haske kan abin da ke faruwa a Gaza a ranar - da kuma halin da fararen hula ke ciki daga hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa da kuma farmaki ta ƙasa.
Kamfanin NetBlocks da ke sa ido ta intanet ya ce "an katse sadarwa a zirin." Katsewar sadarwar na nufin mutane ba su iya tuntuɓar ƴan uwansu - ko kiran motocin ɗaukar marar lafiya ga waɗanda suka samu rauni.
A ranar Lahadi, an dawo da sadarwa, amma a ranar Asabar ba a iya samun mutane da dama a Gaza: Saƙwannin WhatsApp na nuna sun tafi amma ba a karanta ba.
A zantawa ta ƙarshe da muka yi da wani Farfesa a Gaza a ranar Juma'a, ya shaida muna cewa yana fargabar umarnin gargaɗin Isra'ila na ficewa zuwa kudanci, saboda tsoron kada hare-hare su rutsa da iyalinsa kan hanya. Mun kasa samunsa ranar Asabar.
Akwai kaɗan daga cikin mutane a Gaza da ke da layin ƙasashen waje da za a iya samu saboda kusanci da layukan sadarwa na Isra'ila da Masar - Kuma BBC ta yi ƙoƙarin samun wasu lambobin a ranar Asabar.
Sun ƙunshi ɗan jarida a Deir al-Balah, wanda ya bayyana yanayin yankin cikin ruɗani.
"Wasu mutane sun yi imanin cewa babu abin da ke faruwa saboda ba su samun saƙwanni. Hankalinsu ya ɗan kwanta," in ji shi.
"Sauran kuma suna cikin fargaba saboda ba su san halin da ƴan uwansu ke ciki ba."
A arewa mai nisa a Gaza, BBC ta yi ƙoƙarin yin magana da ɗan jarida ta salula. Mutumin wanda aka ɓoye sunansa ya bayyana hare-haren bama-baman da aka kai cikin dare "abin takaici"
"Ba mu yi tunanin za mu kai safe ba," in ji shi, yana mai cewa hare-haren sun shafi gine-ginen gwamnati da wasu filaye da kuma bakin ruwa.
Ba a san asalin adadin yawan waɗanda suka jikkata ba da kuma waɗanda suka mutu tun ranar Juma'a. Hotuna da Bidiyo a ranar Asabar sun nuna yadda aka tarwatsa gidaje da kuma yadda mutane ke ƙoƙarin zakulo mutane a ɓaraguzan gini.
A wani hoton mai tashin hankali, ya nuna wani mutum yana ɗauke da jariri.
A wani bidiyon kuma na daban da aka wallafa a Instagram, an nuna wani mutum da ya ji mummunan rauni ana ƙoƙarin fito da shi da shi a cikin gini da aka tarwatsa yayin da mutane ke kiran a kawo motar ɗaukar marar lafiya.
Maimakon haka, cikin buɗaɗɗiyar mota aka ɗauki mutumin.
A wani saƙon murya, ɗan jarida mai ɗaukar hoto Shebab Younis - wanda ya wallafa bidiyon ya bayyana yanayin da yake gani a matsayin "mummuna.
"Mun kasa ji daga mutanen da aka kai wa hari ko suka jikkata," in ji shi.
"Idan aka kai harin bama-bamai a gidaje, yanayin ya kasance mai matuƙar wahala saboda rashin sadarwa da hanyoyin intanet. Duk wannan yana mummunan illa ga cibiyoyin lafiya da na gine-ginen gwamnati a duk lokacin da aka kai harin bom."
Da aka ƙalubalance shi kan ko Isra'ila ta katse hanyoyin sadarwa a Gaza, Mark Regev babban jami'in gwamnatin Isra'ila, ya shaidawa BBC cewa a ranar Asabar cewa "dama tsari ne a katse sadarwa ga abokan gaba," yana mai cewa Birtaniya da Amurka sun yi a yaƙe-yaƙensu a baya.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce katse sadarwar ta jefa fararen hula cikin "mummunan hatsari."
"Motocin ɗaukar marar lafiya da jami'an kare fararen hula ba su iya kai wa ga waɗanda suka samu rauni, haka kuma akwai dubban mutane da aka ƙiyasta na cikin ɓaraguzan gini," in ji babban jami'in hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
A ranar Asabar, mutane da dama a Gaza sun yi ƙoƙarin isar da saƙon halin da suke ciki ga duniya.
Amma a ranar Asabar yawancin mutanen da ke can, a cewar ɗaya daga cikin waɗanda muke magana da su "duniya ba ta san halin da suke ciki ba."