Everton ta ki sallama tayin da Chelsea ta yi wa Gordon karo na biyu

Anthony Gordon

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Everton ta kara kin sallama tayin fam miliyan 45 da Chelsea ta sake yi wa Anthony Gordon.

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyar Stamford Bridge ta taya Gordon, bayan fam miliyan 40 da ta ce za ta sayi dan wasan tun farko.

Sai dai Everton ta ci gaba da nanata cewar ba za ta sayar da matashin dan kwallon mai shekara 21 ba.

Ana sa ran Chelsea za ta kara kudi a tayi na uku ko Everton za ta amince ta sayar mata da dan wasan.

Gordon ya fara yi wa Everton tamaula a Janairun 2020, wanda a cikin watan Satumba ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar don ci gaba da taka leda a Goodison Park.

Bayan da Dominic Calvert-Lewin ke jinya da sayar da Richarlison ga Tottenham a bana, dan kwallon tawagar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 21 ya yi wa Everton dukka wasa biyu a Premier da ta fafata a kakar nan.

Gordon ya yi wa Everton wasa 51 a Premier League da cin kwallo hudu.