Takardun hukuncin shari'ar Kano sun tada jijiyoyin wuya

b
    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa

A Najeriya an wayi gari cikin yanayi na ce-ce-ku-ce da tafka muhawara dangane da wani kwafin shari'ar da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna cewa kotun ɗauka ƙara ta bai wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf nasara a shari'ar da APC ke kalaubantarsa.

Tun bayan fitar kwafin shari'ar da ake cewa kotun ɗauka ƙara ce ta fitar kan hukuncin da ta yi kan zaɓen gwamnan, ake ta samun mabambanta ra'ayi musamman tsakanin ɓangarori biyun da ke cikin shari'ar.

A ranar Juma'a ne kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja babban birnin ƙasar ta kori ƙarar da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar a gabanta, yana ƙalubanlantar hukuncin da kotun ƙararrakin zaɓe ta yanke.

Kotun ƙararrakin zaɓen ta ce Nasiru Yusuf Gawuna na APC ne ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, ba Abba Kabir usuf na NNPP ba.

Sai dai gwamna Abba Kabir da jam'iyyarsa ta NNPP sun garzaya kotun daukaka ƙarar domin ƙalubalantar hukuncin.

A zaman yanke hukuncin da kotun ta yi ranar Juma'ar da ta gabata dukka alƙalan kotun uku sun ce Nasiru Yusuf Gawana an APC ne ya lashe zaɓen, kasancewar Abba Kabir Yusuf ya yi takarar gwamnan ne ba tare da kasancewa ƙarƙashin inuwar jam'iyya ba.

A ranar Litinin ne kuma kuma jam'iyyar NNPP ta koka kan rashin ba ta takardun kofin hukuncin kotun, tana mai cewa ya kamata a ba ta kofin takardun hukuncin domin lauyoyinta su nazarce su domin ɗaukaka kara zuwa kotu koli.

Me ke kunshe a kwafin shari'ar da ke yawo?

A ranar Talata ne wasu takardu da ke nuna cewa daga kotun suke - wadanda ke dauke da ƙunshin hukuncin suka zo da wani abu na bazata.

Musamman a shafi na 67 na takardun hukuncin.

A shafin alƙalin ya rubuta cewa "Kotu ta samu cewa dukkannin abubuwan da ake ayyanawa a kansu a cikin wannan shari'a ta ɓangaren wanda ake ƙara ne suka yi nasara a kansu''.

Mai ƙara a nan shi ne Abba Kabir Yusuf, yayin da APC da Nasiru Yusuf Gawuna suka kasance wanɗanda ake ƙara.

Kotun ta ƙara da cewa ''Saboda haka wanda ke ƙara shi ne wanda ya yi nasara a kan wanda ake ƙara".

''Don haka ɗaukaka ƙarar da wanda ke ƙara ya yi babu wani dalili ko hujja mai ƙarfi a cikinta, saboda haka an kori ƙarar".

''Saboda haka hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi ranar 20 ga watan Satumba an rushe shi".

''Don haka kotu ta umarci wanda ake ƙara ya biya mai ƙorafi naira miliyan ɗaya a matsayin diyyar ɓata masa lokaci'', kamar yadda takardun hukuncin suka nuna.

e

Asalin hoton, kotu

Wanna shafi na hukuncin ya yi matuƙar tayar da ƙura, inda magoya bayan NNPP da Abba Kabir Yusuf ke ganin hukuncin ya goyi bayansu, saɓanin abin da alƙalan kotun suka bayyana.

Matsayar NNPP

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lauyan jam'iyyar NNPP Barista Bashir Tudun Wazirci, ya ce wannan hukuncin ya nuna cewa kotun daukaka ƙara ta jingine hukuncin farko da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.

Ya ce Hukuncin kotu shi ne wanda kotu ta bayar da shi a rubuce aka kuma sanya masa hannu.

"Yanzu idan kotu na son INEC ta ƙwace takardar shaidar cin zaɓen wani ko ta bayar da shi ga wani, to dole sai an ba ta a rubuce, ba maganar fatar baki ba ce", in ji Lauyan na NNPP.

Ya ƙara da cewa su a wajen su hukuncin ya goyi bayansu kasancewa akwai sa hannun alaƙali da hatimin kotu da kuma babban magatakardan kotun.

Ya ce kalaman ƙarshe na hukuncin kotu shi ne hukunci kan kowace irin ƙara.

''Wannan ba kuskuren alƙalami ba ne, domin shi kuskure ana yinsa ne a wuri ɗaya ko biyu, amma idan aka duba hukuncin, za a ga wajen wuri uku ko hudu duk na nuna cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta yi kuskure", in ji Tudun Wazirci.

Lauyan ya ce babu kamanceceniyar rubuta tsakanin mai ƙara da wanda ake ƙara ballanta a ce an samu kuskuren alƙalami.

Barista Tudun Wazirci ya ce in ba kuskure ba ne, ai kotun ɗaukaka ƙarar ba ta da lokacin da za ta sake komawa ta gyara, kasancewar lokacin da ka ɗaukar mata na kwanaki 60 ya wuce.

Martanin APC

A nata ɓangaren jam'iyyar APC ta bakin lauyanta, Barista Abdullahi Adamu Fagge ya ce su ba su samu takardun hukuncin a hukumance daga kotun ba.

Sai dai ya ce ya ga takardun da ke yawon a shafukan sada zumunta,

"In ma wannan shi ne hukuncin to APC ce da nasara, domin kuwa tun farkon hukuncin mai shafi 72, duka hukuncin goyon bayan jam'iyyar APC yake, sai a feji ɗaya ne wanda shi ma a sakin layi biyu ne kawai aka nuna hukuncin ya goyi bayan NNPP", in ji Barista Fagge.

Lauyan na APC ya ce daga ƙarshe ma hukuncin ya nuna cewa an kori ƙorafin,''kasancewar NNPP ce ta yi ƙorafi, wannan na nuna cewa ƙorafinta aka ƙora tunda ita ta kai ƙorafi".

Ya ce duk wanda ya halarci kotu ciki har da lauyoyin NNPP sun ji irin hukuncin da kotu ta yanke.

"A lokacin da alƙalan ke karanta hukuncin a gaba kotu, babu inda suka yi wannan maganar, kuma duk abin da suka bayyana ya nuna cewa an kori ƙarar da NNPP da ɗan takararta suka shigar, don haka wannan tuntuɓen alaƙalami ne kawai."

'Abin da doka ta ce'

Wani lauya mai zaman kansa a Ingila, Barrista Audu Bulama Bukarti ya ce hukuncin da ya bayyana a shafi na 67 ya zama tamkar tufka da warwara ne, domin kuwa a shafin akwai saɗarori ne guda biyar, inda uku daga ciki suka nuna APC da Nasiru yusuf Gawuna ne suka yi nasara, yayin da guda biyu suka nuna Abba Kabir Yusuf da NNPP ne suka yi nasara.

Barrista Bukarti ya ce duka saɗarorin da ke cikin fejin sun warware junansu.

Lauyan ya ce a doka wannan kuskure ne da ake kira 'Slip Rule' wato tsantsi a dokance.

Ya kuma ce ba a dogara da feji guda wajen fahimtar hukunci, sai an karanta duka abin da hukuncin ya ƙunsa sannan a iya fahimtar hukuncin.

Barrista Bukarti ya kuma ce la'akari da hukuncin, yana nuna cewa Nasiru Yusuf Gawuna da APC su ke da nasara a wannan hukunci ba Abba Kabir Yusfu da NNPP ba.

Yana mai cewa wannan kuskure ba zai sauya hukuncin da kotun ta yanke a lokacin zamanta ba.

Barrista Bukarti ya ce kotun daukaka ƙarar ba ta da hurumin komawa domin gyara hukuncin, kasancewar lokacin da aka dibar mata wajen sauraron shari'ar ya wuce.

"Sannan kuma kuskuren ba ƙarami ba ne, babban kuskure ne, wanda ya munana, don haka sai dai idan NNPP da Abba Kabir sun daukaka ƙara zuwa kotun ƙoli su bayyana wannna korafi a can".

Bukarti ya ce abin da ya kamata Abba Kabir da NNPP su yi shi ne su ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli domin kalubalantar hukuncin da kotun daukaka ƙara ta yi.

Damuwa da ce-ce-ku-ce a kan shari'ar

Sanata Shehu Sani ya ce; 'Kwafin takardun hukuncin da ke yawo, ƙarara sun tabbatar da nasarar gwamna mai ci. Batun Kano abu ne mai sarƙaƙiya, da ke buƙatar kulawa. Tsarin dimokraɗiyyarmu ba zai ci gaba ba, matsawar muna fifita son zuciyar siyasa a kan gaskiya da tsarin mulkinmu".

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Shi kuwa Sambo mai hula cewa ya yi "Ina kira ga abokaina 'yan NNPP da su amince da hukuncin kotu, da ta rushe zaɓen Abba tare da tabbatar da nasarar Nasiru yusuf Gawanu a matsayin halastaccen gwamnan Kano".

"Mu, mutanen jihar Kano, mun yanke hukuncin cewa ba ma son kowa a matsayin gwamnan face Gawuna".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Shi ma wani mai amfani da shafin mai suna Ola Mi Lekan cewa ya yi "Tsarin shari'ar ƙasarmu ya zama abin dariya a duniya".

"Ta yaya za ka yi hukuncin da ya sha bamban da abin de ka rubuce cikin kwafin hukuncin kotun. Wannan abin kunya ne."