Barcelona ta na son ta dawo da Joao Felix, Mourinho zai koma Fenerbahce

Joao Felix

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Sabon kocin Barcelona Hansi Flick yana sha'awar sake ɗauko Joao Felix, mai shekara 24, a matsayin aro daga Atletico Madrid duk da cewa ɗan wasan na Portugal ya kasa samun tagomashi a Nou Camp ƙarƙashin kociyan ƙungiyar da ya gabata Xavi. (Marca)

Jose Mourinho zai sake haduwa da tsohon mataimakinsa Ricardo Formosinho, wanda suka yi aiki tare a Manchester United da Tottenham, bayan ya amince ya zama sabon kocin Fenerbahce. (Telegraph)

Manchester City ta ba da fifiko kan ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan Norway Erling Haaland, mai shekara 23, domin ya ci gaba da kasancewa a filin wasa na Etihad. (Mirror)

Paris St-Germain tana son Napoli ta rage farashin da ta ƙaƙabawa Khvicha Kvaratskhelia daga Yuro miliyan 100 (£85.2m) zuwa aƙalla Yuro miliyan 60 (£51.1m), yayin da take ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan gaba na Georgia mai shekara 23. (L'Equipe)

Monaco ta shirya sayar da ɗan wasan tsakiyar Faransa Youssouf Fofana - wanda Arsenal da Manchester United ke zawarci - a kan fam miliyan 20, a inda ƙwantiragin ɗan wasan mai shekara 25 zai kare a shekara mai zuwa. (Goal)

Ɗan wasan tsakiya na Belgium Axel Witsel, mai shekara 35, ya amince ya jingine batun ritaya daga bugawa ƙasarsa wasa domin buga gasar Euro, kuma yana son sanya hannu kan sabon kwantiragi a Atletico Madrid bayan ya yi nasara a kakar wasan da ta gabata inda ya yi wasa a matsayin mai tsaron baya. (Fabrizio Romano)

Arsenal ta tuntubi Barcelona kan batun sayen ɗan wasan bayan Senegal Mikayil Faye mai shekaru 19. (Mail)

Gunners na son siyan ɗan wasan gaban RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21, kafin ƙarshen watan Yuni. (Florian Plettenberg)

Newcastle na ci gaba da tattaunawa da Bournemouth kan cinikin ɗan wasan bayan Ingila Lloyd Kelly, mai shekara 25, bayan da ta rasa ɗan wasan bayan Fulham da Ingila Tosin Adarabioyo mai shekaru 26, wanda ke shirin komawa Chelsea. (Sky Sports)

Dan wasan bayan Holland Sepp van den Berg, mai shekara 22, ya buƙaci Liverpool ta cefanar da shi a wannan bazarar. (De Telegraaf)