An sace lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ta tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu FW de Klerk a gidansa

Asalin hoton, AFP
An sace lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ta tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu FW de Klerk daga gidansa a watan Afrilu, kamar yadda gidauniyarsa ta tabbatar wa BBC.
Ba ta yi karin haske ba amma kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa an sace lambar yabon ne a lokacin da aka yi fashi a gidansa da ke Cape Town.
Mista De Klerk ya lashe kyautar tare da Nelson Mandela a shekarar 1993 saboda kokarin da suka yi na kawo karshen wariyar launin fata.
Kafofin yada labaran Afrika ta Kudu sun ruwaito cewa ‘yan sanda ba su kama wani ko gano lambar yabo ba
A hirar da ta yi da wata kafar yada labarai ta intanet da ake kira News24 matar marigayin, Elita ta ce ta dawo gida daga balaguron da ta yi a kasashen ketare sai ta ga wurin da suke ajiye kayayakin su masu muhimanci kusan “an yi masa kat”
" Na fahimci cewa an yi mana sata ne a watan Afrilun bana .A ranar 5 ga Afrilu, na je wurin da mu ke ajiye kaya, inda na sameshi a bude. Na dawo daga wata ziyarar da na kai ketare a ranar 4 ,shi yasa na iya tunawa da ranakun kwanakin kuma abin takaici shi ne kusan komai aka kwashe”. In ji ta
"An kwashe kayan ado na da yawa - da wuya na san kudin kayan saboda kayan adon da aka dauka an bani su ne a cikin shekaru 50 da suka gabata kuma akwai wasu kayayki da na gada daga wurin mahaifiyarta,," ta kara da cewa .
Ta ce ba ta da kwarin gwiwar cewa za a gano kayayakin da aka sace.

Asalin hoton, AFP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tare da Mista Mandela wanda shi ne bakar fata na farko daya zama shugaban kasar Afrika ta kudu aka Mista De Klerk wanda ya mutu a shekarar 2021 kyautar tare da zinariya mai nauyin karat 18 a 1993.
A shekarar 1989 Mista de Klerk ya zama shugaban kasa amma ya mikawa Mista Mandela mulki shekaru biyar bayan haka. Abinda kuma ya kawo karshen mulkin fara fata da ba su da rinjaye a kasar kuma ya bude sabon babi a mulkin dimukradiyyar kasar.
Ya mutu kusan shekara daya da ta gabata yana da shekara 85 sanadin cutar daji da ta shafi huhu.
A farashin zinari na yanzu darajar zinarin mai nauyin karat 18 ya kai dala dubu 7 da dari uku amma ana ganin darajar ta fi haka.
A watan Yunin daya gabata dan jarida dan kasar Rasha Dmitry Muratov wanda shi ma an ba shi kyautar lambar yabo a 2021 ya sayarda nasa a kan kudi dala miliyan 103 domin ya tara kudi ga yara 'yan Ukraine da ke gudun hijira.
Haka kuma a shekarar 2014 masanin kimiya ba'Amurke nan James Watson ya yi gwajon nasa a kan kudi fiye da dala miliyan 4









