Dudula: Yadda 'yan Afirka ta Kudu ke huce fushinsu a kan baƙi a ƙasar

People on a demonstration

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A farkon makon jiya mazauna Alexandra sun yi zanga-zanga inda suke kira ga 'yan kasashen waje su fice daga birnin
    • Marubuci, Daga Pumza Fihlani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Johannesburg
  • An wallafa

'Yan sanda a Afrika Ta Kudu na cikin shirin ko-ta-kwana na barkewar sabon rikici tsakanin mazauna birnin Johannesburg na unguwar Alexandra da kuma masu yasar da kaya a kan titi yan kasashen waje.

Alexandra na daya daga cikin unguwanni a kasar masu fama da talauci amma daga cikin bukkokin unguwar, mazauna yankin na iya gano tsayin ginin Sandton daya daga cikin yankunan kasuwanci a duka Afrika, kilomita kadan ne tsakani. A sakamakon haka mutane a ciki da wajen kasar na amfani da unguwar a matsayin wurin zama da ke mafi kusa domin samun abubuwan rayuwa.

Wasu kungiyoyi biyu masu rudani da ake kira Alexandra Dudula da kuma Operation Dudula - sun kunno kai kuma abin da suke yi shi ne yaki da 'yan kasashen waje da ke zaune a kasar ba da takardu ba, kuma suna kara samun goyon baya a kasar musamman daga mutanen da suke jin ba a yi musu adalci.

Ana fargabar wannan fafutukar tasu za ta iya haifar da wata fafutukar yaki da launin fata da ta haifar rikici a kasar a baya.

Me wadannan kungiyoyi ke so?

'Yan Afrika Ta Kudu sun yi amannar cewa talauci ne ke kara ingiza halin da ake ciki - ko daidai ne ko ba daidai ba - 'yan kasar wajen na cikin abubuwan da ke ta'azzara halin matsin da ake ciki.

Kalmar Dudula kalmar yaren Zulu ne wadda ke nufin "turawa baya" ko kuma "mayarwa" - wannan kuma ya dan ba da kafar gano me suke nufi.

Duk da cewa duka kungiyoyin zaman kansu suke, amma manufa daya suka kafu a kai - dukan su suna son korar bakin kasashen waje da ke zaune a kasar ba tare da takardu ba daga unguwanninsu.

Sun yi amannar cewa idan hakan ta faru kuma ayyuka da damar kasuwancin da suka mamaye za su koma hannun 'yan Afrika Ta Kudu.

Mene ne bambancin kungiyoyin biyu?

An kafa Alexandra Dudula Movementa a bara. 'Ya'yan kungiyar na zargin cewa 'yan kasashen waje sun mamaye gidajen da gwamnati ta gina ta ba da haya cikin sauki a unguwar Alexandra, wadanda aka gina saboda talakawan kasar.

Mutanen na wakar cewa baki su 'tafi gida'

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Alexandra Dudula na zargin 'yan kasashen waje ne ke zaune a gidajen gwamnati da aka sanya wa tallafi

Amma wannan fafutukar ta kara samun karbuwa kuma yanzu ana sanar da cewa 'yan kasashen Afrika da ke kasar su daina kasuwanci a Alexandra. A watan jiya wannan fafutukar ta kara fadada zuwa kan wasu 'yan kasar wadanda ba sa iya nuna takardu masu kyau da suke yin kasuwanci da kuma fasfo mai kyau.

Sun kuma fara raba wa 'yan Afrika ta Kudu shaguna, kamar mazauniyar yankin Alexandra Wendy Sithole, wadanda suka fara sayar da kayan gona lokacin da aka kori 'yan kasar wajen karfi da yaji.

"Mu ba mu da ayyukan yi kuma muna fama da yunwa. Abin da muke bukata mutanenmu su samu ayyukan yi," ta gaya wa BBC."Yaya suke zaton za mu rayu a kasarmu?

Ba ko wanne mataki da kungiyar ta dauka ba ne yake zama ya yi dai-dai da shari'a kuma hukumomi na bincike kan rikicin da ake samu da kuma barazana.

Operation Dudula na garin Johannesburg a unguwar Soweto - sama da kilomita 25 daga birnin.

Wani matashi ne dan shekara 33 Nhlanhla Lux Dlamini ya kafa ta, a watan Yuni ne kuma ta samu karbuwa ta yi shuhura yayin da mazauna Soweto suka yi wani maci a duka fadin yankin wanda suka kira da "shara".

An yi shi ne saboda wadanda ake zargi da safarar kwayoyida kuma wadanda ke zaune a muhallan da gwamnati ta gina ba bisa ka'ida ba.

Kamar dai a Alexandra, kungiyar ita ma muradanta sun fadada.

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A watan jiya mambobin OD sun yi maci a Soweto

Mambobin na bukatar masu shaguna 'yan kasashen waje su rufe kasuwancin nasu su bar kasar.

Kuma suna son masu kananan kasuwanci irinsu dakunan sayar da abinci da shaguna su rika daukar 'yan Afrika Ta Kudu kawai. Saboda masu fafutukar sun yi amannar cewa wadannan wuraren na kawar da kai kan 'yan Afrika Ta Kudu su bai wa 'yan kasashen wajen da za su biya su kudade masu yawa.

Hukumomi sun ce ba a ko'ina wannan abin ke faruwa ba.

Duka kungiyoyin biyu sun musanta cewa suna yi ne domin nuna kin jinin 'yan kasashen ketare, suna cewa suna yi ne domin kare muraden 'yan Afrika Ta Kudu, Abin da suka zargi jam'iyyar ANC da gaza yi.

Duka biyun sun ce ba su da wata alaka da jam'iyyar siyasa.

Wane martani ake mayarwa?

Daga 'yan kasashen waje suna cewa ana dora musu zargin kan wannan matsaloli.

"Ba mu hana kowa samun aiki ba, mu muka samarwa kanmu ayyuka, ba mu kuma hana 'yan Afrika Ta Kudu yin abin da muma muke yi ba," in ji Sam Manane wani dan kasar Mozambique da ke sayar da kayan makwalashe a Alexandra sama da shekara 10.

"Kawai dai suna neman cutar da mu."

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu masu shago na ta rufe shagunansu domin kaucewa rikici.

Har yanzu gwamnatin tarayyar kasar ba ta ce komai kan wannan batu ba, sai dai ta yankin Gauteng ciki har da ta Juhannesburg da kuma David Makhura na ANC sun nuna damuwa kan wannan tashin hankali. Kuma ya yi kira ga kungiyoyin fararen hula su yi aiki tare da gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya da hakurin zama da juna.

Amma wasu jam'iyyuna adawa na neman kokarin cin moriyar wannan rikici da ake yi.

A farkon wannan shekarar, wasu mambobin hukumar da ke lura da kasuwanci ta kai ziyarar ba-zata wajen wasu gidajen cin abinci domin ganin yawan 'yan Afrika ta Kudu da ke aiki a wajen.

Me ya sa wannan ke faruwa?

Ba wannan ne karon farko ba da ake samun guguwar nuna kin jinin 'yan ksashen waje a Afrika ta Kudu.

A 2008, An samu wani mummunan hare-hare kan 'yan gudun hijira da 'yan cirani - sama da mutum 60 aka rawaito cewa an kashe yayin da dubbai suka yi batan dabo.

An kara samun wata a 2015, kan wadanda ba 'yan Afrika Ta Kudu ba, mafi yawa a yawa a biranen Durban da Johannesburg.

A shekaru uku da suka gabata an samu irin wadannan hare-hare da suka tilasta wa daruruwan 'yan Najeriya barin kasar ba tare da shiri ba.