Dukkan kyautukan da aka lashe a Afcon 2023 a Ivory Coast

Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Lahadi aka kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka, inda Ivory Coast ta lashe kofin kuma karo na uku jimilla.

Mai masaukin baki ta yi nasarar cin Super Eagles 2-1 a karawar da suka buga a filin wasa na Alassane Ouattara.

Najeriya ce ta fara cin ƙwallo ta hannu William Troost-Ekong tun kafin a je hutun rabin lokaci, sai dai bayan da suka koma zagaye na biyu ne Ivory Coast ta farke ta hannun Franck Kessie da kuma Sebastien Haller.

Kofi na uku ke nan da Ivory Coast ta lashe, bayan wanda ta ci a 1992 da kuma a 2015.

Ɗan wasan Ivory Coast, Simon Adingra shi ne ya lashe kyautar wanda ya fi taka rawar gani a wasan karshe a Afcon ranar Lahadi.

Ƙyaftin din Najeriya, William Troost-Ekong shi ne aka bai wa ƙyautar fitaccen ɗan wasan gasar baki ɗayan ta.

Ɗan wasan tawagar Equatorial Guinea, Emilio Nsue Lopez shi ne ya karbi ƙyautar takalmin zinare a matsayin wanda ya fi cin ƙwallaye - guda biyar a raga.

Haka kuma golan Bafana-Bafana, Ronwen Williams shi ne mai tsaron ragar da babu kamarsa a gasar kofin Afirka da aka kammala a Ivory Coast.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya karbi kyautar ne bayan buge fenariti hudu a wasa da Cape Verde da kuma biyu a karawa da DR Congo ta kai Afirka ta Kudu ta ƙare a gurbi na uku.

Bayan da Afirka ta Kudu ta yi ta uku a Afcon a bana, ita ce ta karbi kyautar wasa ba da gaba ba da ake kira Fair Play.

A lokacin bikin da aka yi ranar Lahadi, ɗan kwallon Togo, Emmanuel Adebayor ne ya fito da kofin Afirka filin wasa domin bai wa Ivory Coast.

Haka kuma shugaban kasa, Alassane Ouattara tare da shugan CAF, Dr Patrice Motsepe da na FIFA, Gianni Infantino ne suka miƙa kofin ga kyaftin ɗin Ivory Coast, Max Gradel.

Haka kuma an yi bikin bai wa hukumar ƙwallon kafar Morocco tuta da cewar ita ce za ta shirya wasannin da za a yi a 2025 - gasa ta 35.

Ga jerin wadanda suka lashe ƙyautuka a Afcon 2023 a Ivory Coast 2023

Wadda ta lashe kofin: Cote d’Ivoire

Wadda ta yi ta biyu: Najeriya

Wadda ta kammala a mataki na uku: Afirka ta Kudu

Wadda ta yi ta hudu: Jamhuriyar Dumukraɗiyyar Congo

Fitatcen ɗan wasan gasar: William Troost-Ekong (Najeriya)

Wanda ke kan gaba a cin ƙwallaye: Emilio Nsue Lopez

Fitatcen mai tsaron raga: Ronwen Williams (Afirka ta Kudu)

Wasa ba da gaba ba: Afirka ta Kudu