Liverpool ta zura kwallo 4-1 a ragar Brentford a Premier

Mohammed Salah

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool ta bayar da tazarar maki biyar a teburin Premier League, bayan da ta je ta dura 4-1 a ragar Brentford wasan mako na 25.

Kungiyar Anfield ta fara cin kwallo ne ta hannun Darwin Nunez, saura minti 10 a tafi hutun rabin lokaci kuma a haka aka je aka dawo.

Tun kan nan kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ta yi sauyin ƴan wasan, inda Mohamed Salaha ya canji Jota a minti na 44, sannan Gakpo ya maye gurbin Darwin Nunez a minti na 45.

Daga nan Liverpool ta ci gaba da kara zura ƙwallo a raga ta hannun Alexis Mac Allister, sannan Mohamed Salah ya ci na uku.

Ƙwallon da Salah ya ci shi ne na farko da ya zura a raga tun shiga sabuwar shekara a Premier League.

Salah ya koma buga wa Liverpool tamaula, bayan jinya da ya yi lokacin da ya ji rauni lokacin da ya ke buga wa ƙasarsa Masar gasar cin kofin Afirka a Ivory Coast.

Brentford ta zare daya ta hannun Ivan Toney saura minti 25 lokaci ya cika, sai dai kuma Liverpool ta zura na biyar saura minti hudu a tashi ta hannun Cody Gakpo.

Manchester City za ta iya rage tazarar maki da ke tsakaninta da Liverpool ya koma biyu da zarar ta yi nasara a kan Chelsea a ranar ta Asabar.

Haka itama Arsenal wadda take ta ukun teburi za ta iya rage tazarar zuwa maki biyu tsakaninta da ta Anfield, idan ta doke Burnley.

Premier

Asalin hoton, BBC Sport

Ko da ya ke ƴan wasan Liveerpool sun yi rauni a karawa da Brentford, yayin da Curtis Jones da Diogo Jota aka sauya su.

Haka shi ma Nunez sai hakura ya yi da fafatawar.

Mohamed Salah da Cody Gakpo sun zama na biyu a tarihin Premier League da suka sauyi ɗan wasa, sannan suka ci ƙwallo, kuma ko wanne ya bayar aka zura a raga.

Masu wannan ƙwazon sune ƴan wasan Arsenal, Aubameyang da Ramsey a karawa tsakanin Gunners da Fulham cikin Oktoban 2018.

Haka kuma Salah ya ci kwallo ya kuma bayar an zura a raga karo na 30 a Premier League.

Wadanda ke gabansa a irin wannan bajintar sun hada da Wayne Rooney mai 36 da Thierry Henry mai 32 da kuma Alan Shearer mai shekara 31.