Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema ya koma atisaye a Real Madrid bayan jinya da ya yi
Real Madrid ta fara atisaye a shirin da take na fuskantar wasan La Liga karawar mako na bakwai da za ta karbi bakuncin Osasuna ranar Lahadi.
Cikin wadanda suka yi atiaye a safiyar nan har da dan kwallon tawagar Faransa, Karim Benzema, wanda ya sha jinya.
Dan kwallon ya ji rauni a wasan da Real Madrid ta je ta doke Cetic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar 6 ga watan Satumba.
Benzema, wanda ya buga wa Real Madrid wasa biyar har da Champions League daya a bana ya ci kwallo uku.
Dan wasan ya yi atisaye karkashin Ancelotti ranar Laraba, wanda ya samu halartar wasu 'yan kwallon, bayan da suka buga wa tawagoginsu wasanni.
Wadanda suka koma atisaye har da Courtois da Hazard da Camavinga da Alaba da Mendy da Tchouameni da kuma Rudiger.
Lucas Vázquez na ci gaba da murmurewa, yayin da Modric ya motsa jiki a rufaffen daki.
Wasannin da Real Madrid za ta buga nan gaba
Spanish La Liga Lahadi 2 ga watan Oktoba
- Real Madrid da Osasuna
Champions League Laraba 5 ga watan Oktoba
- Real Madrid da Shakhtar
Spanish La Liga Asabar 8 ga watan Oktoba
- Getafe da Real Madrid
Champions League Talata 11 ga watan OOktoba
- Shakhtar da Real Madrid
Spanish La Liga Lahadi 16 ga watan Oktoba
- Real Madrid da Barcelona