Juventus za ta kara yi wa Pogba gwaje-gwaje kan raunin da yake dauke da shi

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Juventus ta sanar cewar Paul Pogba ya ji rauni a gwiwar kafarsa, za ta hada shi da kwararren likita, domin fayyace girman raunin.

Raunin ne ya sa bai buga wasan sada zumunta da kungiyar ta yi da Barcelona a Dallas ranar Talata ba.

Mai shekara 29, ya sake komawa kungiyar a karo na biyu a bana, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Manchester United a karshen kakar da ta wuce.

Juventus ta ce Pogba ya sanar cewar "Ina jin radadi a gwiwar kafata ta hagu" kuma gwajin da aka yi masa ''an gano raunin da ya ji''.

Kungiyar ta kara da cewar: ''Nan da wasu awanni zai gana da kwararren likita.''

''Saboda haka, zai ci gaba da samun kulawa, ba zai je wasan da za mu kara a Dallas ba.''

Pogba ya yi wa Juventus wasan sada zumunta daya shi ne wanda ta doke kungiyar Mexico, Chivas Guadalajara 2-0 a Las Vegas.