Lafiya Zinariya: Haɗarin bijirewa magungunan kashe kwayoyin cuta
Lafiya Zinariya: 03/08/2024
Ƙwayoyin cuta na ci-gaba da bijirewa magungunan da ke kashe su, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 1.27 miliyan a fadin duniya, a shekarar 2019, a cewar hukumar lafiya ta duniya.
Matsalar ta fi ƙamari ne a ƙasashe masu ƙaranci da matsakaicin kuɗin shiga. Inda ake samun kashi 90 cikin ɗari na mutuwar da ake samu kai tsaye sakamakon wannan matsalar.
Wani binciken da aka yi a Najeriya, kasancewarta ɗaya daga cikin ƙasashen yammacin Afrika da ke fama da matsalar ya nuna cewa, wannan yanayi ya kai ga mutuwar fiye da mutane 64,000 a shekarar 2019.
Yayin da wasu kimanin 200,000 mutuwarsa ke da alaƙa da bijirewar da kwayoyin cuta ke yi wa magungunan.
Likitoci a ƙasar sun bayyan cewa shan magungunan kashe ƙwayoyin cuta barkatai ba tare da wani izini daga likita ba ya taimaka wajen jefa al'umma cikin matsalar bijirewa magungunan da kwayoyin cutar ke yi.
Haka kuma masu kiwon dabbobi kamar shanu, akwaki, tumaki, kaji da sauransu na bai wa dabobin irin waɗannan magunguna domin su ƙara girma, lamarin da ke jefa mutane cikin haɗari musamman idan an yanka dabbar ba tare da ta cika lokacin da ya kamata a ce maganin ya gama amfani a jikinta ba.
Hukumar lafiya ta WHO ta bayyana matsalar a matsayin gagaruma a fannin kiwon lafiyar duniya, kuma ba ta tsaya kan bil'adama da dabbobi ba, har ma ta shafi tsirrai, inda take rage amfanin gona, lamarin da ke haifar da barazana ga samar da abinci.