Shin da gaske an murɗe sakamakon zaɓen Kenya?

Asalin hoton, Getty Images
An ayyana William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Kenya tun mako biyu da suka gabata bayan da ya tashi da kashi 50.5% na ƙuri'un amma abokin hamayyarsa Raila Odinga ya ƙalubalanci zaɓen inda ya yi iƙirarin an tafka maguɗi.
Lauyoyin Mista Odinga sun lissafa rumfunan zaɓe fiye da 40 inda suka ce an murɗe zaɓen domin ƙara wa Mista Raila ƙuri'u domin kai su zuwa kashi 50% da ake buƙata ya lashe zaɓe.
Mun haɗa sakamakon da aka fitar a hukumance daga rumfunan zaɓen daga waɗan nan rumfunan zaɓe tare da waɗanda hukumar zaɓe ta yi rajista a shafinta na intanet.
Mene ne zargin?
A Kenya, da zarar an kammala zaɓe aka kuma ƙirga ƙuri'u, Baturen Zaɓe a kowace rumfar zaɓe yana sanar da sakamakon zaɓen a bainar jama'a tare da cike fom 34A don tabbatar da wanda ya lashe zaɓe.
Wakilan Jam'iyyar na rattaba hannu a jikin fom ɗin kafin tura sakamon zaɓen ta intanet zuwa cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta ƙasa da hukumar zaɓen ta samar a intanet.

Asalin hoton, Getty Images
Lauyan Mr Odinga ya ce a rumfunan zaɓe 41 an ɗora sakamakon zaɓe domin ƙara yawan ƙuri'un Mista Ruto kafin hukumar zaɓe ta buga a intanet. Ga wani ɓangare na koen da aka shigar gaban Kotun Koli inda aka yi zarge-zargen:
- Yawan ƙuri'un da mai ƙorafi na farko da wanda ake ƙara a fom ɗin 34A da aka shigar kan wakilai a rumfunan zaɓe, ya sha banban da Fom 34A da ke shafin IEBC.
- A Dukkan foma-foman 41 da ke shafin IEBC, an rage ƙuri'un mai gabatar da ƙorafi yayin da aka yi wa ƙuri'un wanda aka ƙara aringizo don yawan ƙuri'un ya zama bai sauya ba.
Takardar ƙorafin na iƙirarin an sauya takardun tabbatar da zaɓen domin nasarar Mista Ruto. An sauya yawan ƙuri'un, ana tabbatar da cewa ƙuri'un da aka kaɗa bai sauya ba.
Takardar ƙorafin ta nuna cewa an tafka maguɗi a kwafin sakamakon zaɓen na intanet bayan da aka turo su daga rumfunan zaɓe.
Abin da muka gano
Sai muka yanke shawarar duba ainahin samakon zaɓn daga rumfunan zaɓe domin gano ko sun banbanta daga foma-foman da aka wallafa a intanet.
Mun gano cewa duk fom ɗin da aka rattaba wa hannu yana ɗauke da lambar waya ta wakilan Jam'yya da suke wajen a lokacin da ake ƙirge.
Waɗan nan wakilan Jam'iyyar da suka sa ido kafin kirga ƙuri'un domin tabbatar da komai ya tafi da-dai.
Mun kuma fara kiransu ɗaya bayan ɗaya domin tambayarsu ko sun ɗauki hotunan sakamakon zaɓen a lokacin da aka sanar da sakamakon - idan kuma haka ne, za su iya tura mana.

Asalin hoton, Getty Images
Mun samu martani daga wakilai 23 ciki har da shida daga haɗakar Mista Odinga da hotunan ainahin fom ɗin daga rumfunan zabe 21 cikin 41 da aka gano.
Wakilai biyu sun bamu bayanan da suka rubuta a lokacin amma babu hotuna.
Sakamakon zaɓen daga rumfunan zaɓe ya yi dai-dai da sakamakon zaɓen da hukumar zaɓen ta bayyana.
Hotunan foma-foman

Asalin hoton, others
A ƙasan kowace takarda akwai sunaye da yawan wakilan da suke wajen. Mun rufe waɗan nan wuraren domin kare su.
Sun ɗauki hoton takardar sakamakon zaɓe ta ƙarshe kuma sune mutanen da muka tuntuɓa daga rumfunan zaɓe 41 da tawagar Mr Odinga suka bayyana.

Asalin hoton, others
Burinmu a wannan maƙala shi ne gano hujja ta goyon bayan iƙirarin Mr Odinga na katsalandan kuma mun gaza samun shaida.
Mun tuntuɓi tawagar Mista Odinga domin samar da shaida kan zargin tafka maguɗi amma ba mu ga komai ba.
Kotun Kolin Kenya na dab da yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar nan da ƴan kwanaki.










