Barcelona ta amince za ta dauki Kounde daga Sevilla

An wallafa

Barcelona ta amince za ta dauki dan kwallon tawagar Faransa, mai tsaron baya, Jules Kounde daga Sevilla kan kudi da aka ce ya kai fam miliyan for 41.85.

Koda yake Barcelona ta ce za ta kammala cinikin idan an kammala auna koshin lafiyar dan kwallon mai shekara 23.

Mai tsaron bayan ya yi wasa 133 a Sevilla da lashe Europa League a kakar farko, bayan da ya koma Sifaniya daga Bordeaux a 2019.

Ya kuma buga karawar da tawagar Faransa ta doke Sifaniya 2-1 a bara a wasan karshe a Nations League.

Bayanda Kounde zai koma Camp Nou a kakar nan, tuni Barcelona ta dauki 'yan wasa da suka hada da Robert Lewandowski daga Bayern Munich kan fam miliyan 42

Ta kuma dauki dan wasan Brazil, Raphinha daga Leeds United kan fam miliyan 55.

Haka kuma ta dauki dan wasan da yarjejeniyarsa ta kare a AC Milan, dan kwallon Ivory Coast, Franck Kessie.

Ta kuma dauki dan wasan tawagar Denmark mai tsaron baya, Andreas Christensen, wanda kwantiraginsa ya kare a Chelsea.

Tuni kuma dan wasan tawagar Faransa, Ousmane Dembele ya sa hannu kan tsawaita zamansa a Barcelona.