Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan hafsoshin Ecowas sun buɗe taron Ghana don tunkarar Nijar
Manyan hafsoshin sojin Ecowas sun buɗe wani taro a Ghana don shiryawa kan yiwuwar tura dakarun mamaye cikin ƙasar Nijar, da nufin dawo da mulkin dimokraɗiyya.
Kwamishinan harkokin zaɓe da tabbatar da zaman lafiya da tsaro na Ecowas, Abdel-Fatau Musah ya ce kusan duk ƙasashe mambobin ƙungiyar sun yi alƙawarin ba da gudunmawar dakaru, sannan a shirye suke su mamaye Nijar.
Janar Abdurrahamane Tchiani ne ya hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed a wani juyin mulki cikin watan Yuli.
Taron na zuwa ne bayan da shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma sun umurci rundunar sojin ƙasashen Ecowas, ta kasance cikin shirin yaƙi.
A yanzu a bayyane take cewa ECOWAS ta ƙara ƙaimi a kan barazanar amfani da ƙarfin soja domin mayar da Nijar kan turbar dimokraɗiyya tun bayan juyin mulkin sojoji a watan Yuli.
Manyan hafsoshin ECOWAS za su tsara dabarun da za a yi amfani da su wajen amfani da ƙarfin soja a jamhuriyar Nijar.
Za su kuma tattauna kan yawan kayan yaƙi da adadin sojojin da ake buƙata da kuma tsarin da sojojin za su bi a Nijar.
Ecowas tana ƙara matsa lamba kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar bayan ƙoƙarin diflomasiyya ya samu tangarɗa.
Manyan hafsoshin a yanzu na ƙarfafa tsare-tsare kan yiwuwar mamaye Nijar.
Jami'an Ecowas sun ce za su yi amfani da dukiyarsu wajen tallafa wa dakarun, amma za su yi maraba da duk wani taimako da za su samu daga waje.
Sojoji masu juyin mulki sun keta dokokin Ecowas game da shugabanci nagari da tsarin dimokraɗiyya lokacin da suka ƙwace iko a watan jiya, kuma ƙungiyar ƙasashen yankin ta ƙuduri aniyar mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan kujerarsa.
Nijar, ƙasa mai arziƙin yuraniyam na ɗaya daga ƙasashe mafi talauci a duniya kuma tana fama da mummunan rikicin masu iƙirarin jihadi. Akwai damuwar cewa duk wani ƙarin tashin hankali zai iya ta'azzara halin taɓarɓarewar tsaro a ɗaukacin yankin Sahel.
A baya, dakarunn Ghana da Najeriya sun jagaronci ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya a yankin na Afirka ta Yamma ƙarƙashin rundunar ECOMOG a ƙasashen Laberiya da Saliyo a shekarun 1990.
Ƙungiyar ta kuma shiga tsakani a wasu ƙasashe mambobin ƙungiyar inda ta baya-baya nan ita ce Gambiya.
Sai dai, kawunan mambobin kungiyar ya rabu gida biyu game da amfani da ƙarfin soji a jamhuriyar Nijar, sannan ga dukkan alamu Tarayyar Afirka ta zaɓi hanyar amfani da kafar diflomasiyya.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar taɓarɓarewar tsaro a Nijar.
Sojoji 17, aka kashe yayin da 20 suka jikkata a harin kwanton-ɓauna da mayaƙa masu iƙirari jihadi suka kai ranar Talata.
Shi ne hari na bakwai da aka kai wa dakarun Nijar, tun bayan juyin mulki kuma shi ne mafi muni.
Gwamnatocin yankin sun damu da cewa tashin hankalin zai iya bazuwa zuwa ƙasashensu.
An kashe fararen hula a wani harin daban
Aƙalla mutum 31, rahotanni suka ambato cewa sun rasu ranar Talata da yamma, a jerin hare-haren da aka kai a kan wasu ƙauyuka da ke yankunan Dessa da Mehanna na jihar Tillabéri.
Majiyoyi sun ce wasu mutane ne ɗauke da makamai da ake kyautata zaton mayaƙan ƙungiyar IS na yankin Babbar Sahara (EIGS) ne suka auka wa ƙauyukan Tomare da Issile da Gaberi da Kodogoria.
An kai hare-haren ne a rana ɗaya da mummunan harin kwanton-ɓaunan da wasu mahara suka wa ayarin sojojin Nijar a tsakanin Torodi da Boni, inda suka yi sanadin kashe soja 17, wasu 20 suka jikkata.
Hukumomi sun ce an kuma kashe 'yan bindiga 100.
Wannan dai shi ne karon farko a jerin hare-hare guda takwas da 'yan bindiga suka far wa fararen hula tun bayan da Nijar ta auka cikin hargitsin siyasa a yankin Tillabéri na kan iyaka uku.
Dr Zirbine Abass na ƙungiyar Action for Humanity dai ya koka da faruwar wannan lamari. A cewarsa, tashe-tashen hankula a kewayen Kogin Isa musamman a yankin na Tillaberi.
Ya ce kamar yadda suka lura, al'amarin sai daɗa rincaɓewa yake yi, inda ya yi iƙirarin cewa matsalar ta’addanci na rikiɗewa tana ɗaukar wani abu daban.