Matsi zai dan sauka daga kan Ten Hag bayan cin Burnley

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta je ta doke Burnley 1-0 a wasan mako na shida a Premier League da suka fafata a Turf Moor ranar Asabar.

Kungiyar Old Trafford ta ci kwallon ta hannun kyaftin, Bruno Fernandes, hakan ya ba ta maki ukun da take bukata.

United ta hada maki tara, bayan doke Wolverhampton da Nottingham Forest da kuma Burnley.

Yayin da ta yi rashin nasara a hannun Tottenham da Arsenal da kuma Brighton daga wasa shida da ta fafata.

United tana buga kaka mafi muni da fara Premier League, wadda rabon da ta yi rashin kokari irin haka tun bayan shekara 37.

A lokacin ta yi rashin nasara a wasa hudu daga shida da fara buga babbar gasar tamaula ta Ingila a dukkan fafatawa wato a 1986.

Ta kuma yi rashin nasara a wasa biyu da ta kai ziyara a bana da suka hada da wanda Tottenham ta doke ta da na Arsenal.

Rabon da hakan ya faru a United tun a 1973/74 kakar da kungiyar ta fadi daga Premier League kenan.

An zura kwallo 14 a ragar kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama a dukkan fafatawa kan wasa da Burnley, ita ce aka ci kwallaye da dama a gasar a bana.

Haka kuma an zura kwallo uku ko fiye da haka a ragar kungiyar Old Trafford karo uku a jere a karon farko da hakan ya faru da ita tun daga Disambar 1978.

Kafin United ta fuskanci Burnley ta yi nasara karo 17 daga wasa 24 da ta fuskanci sabbin kungiyoyin da suka hau Premier League.

Wasa biyu Burnley ta yi nasara a kan United daga 16 baya da suka kara da yin canjaras biyar aka doke ta tara kafin wasan na ranar Asabar.

Burnley ta kasa cin United a fafatawa takwas a Turf Moor da canjaras biyar.

Ranar Talata 26 ga watan Satumba, United za ta fafata da Crystal Palace a League Cup, sannan su kara fuskanta juna kwana hudu tsakani a Premier.

Karawa ta gaba da United za ta yi shi ne karbar bakuncin Galatasaray a Champions League, sai ta kece raini da Brentford daga wasa hudun da ke gabanta.