Jamus ta kai kwata fainal a Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images
Jamus ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe, bayan da ta doke Denmark 2-0 ranar Asabar a Signal Iduna Park.
Tawagar ta fara zura ƙwallo a raga ta hannun Kai Havertz a bugun daga kai sai mai tsaron raga, Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne.
Mai masaukin baƙi ta samu bugun fenariti, bayan da Joachim Andersen ya taɓa ƙwallo da hannu a bugun da David Raum ya yi.
Daga baya ne Jamus ta kara na biyu a ragar Denmark ta hannunn Jamal Musiala, wanda ya ci na uku a Euro 2024.
Ya fara ci wa Jamus ƙwallo a wasa da Scotland da suka ci 5-1 da kuma a karawa da da Hungary da aka doke 2-0.
Wani ɗan ƙwallon da ya zura uku a raga a Euro 2024 shi ne Georges Mikautadze na Georgia.
Tun farko dukkan tawagar biyu kowacce ta ci ƙwallo, amma aka soke, bayan da aka tuntuɓi na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci.
Tun kan karawar Denmark da Jamus sun haɗu sau hudu a manyan gasar tamaula, fitatciyar karawar da suka ita ce a Euro 1992 a Gothenburg, inda Denmark ta ci 2-0.
Alkalan Ingila ne suka ja ragamar wasan, inda Michael Oliver ya busa karawar, masu labule kuwa sun hada da Stuart Burt da kuma Dan Cook.
Wadanda suka kula da na'urar VAR kuwa sun hada da Stuart Atwell da kuma David Coote.
Da wannan sakamakon Jamus za ta buga daf da na kusa da na karshe da duk wadda ta yi nasara tsakanin Sifaniya da Georgia, wadanda za su fafata ranar Lahadi.
Denmark ta kafa tarihin zuwa zagaye na biyu ba tare da cin wasa ba a rukuni
Denmark ta kafa tarihin kai wa zagaye na biyu ba tare da nasara ba a wasannin cikin rukuni da ta buga a Euro 2024.
Tawagar da take rukuni na uku ta tashi 1-1 da Slovenia da yin 1-1 da Ingila da kuma 0-0 da Serbia.
Ita ce ta yi ta biyu a rukuni na uku da maki uku, kenan ta farko da ta yi wannan bajintar a rukuni zuwa zagayen ƴan 16 ba tare da cin ƙwallo ba.
Tawagar Ingila ce ta ja ragamar rukuni na uku da maki biyar, wadda za ta kece raini a zagaye na biyu da Slovekia ranar Lahadi.
Haka itama Slovenia ta yi canjaras uku a karawar cikin rukuni a Euro 2024, kamar yadda Denmark ta yi a rukuninsu na uku.
Portugal ta taɓa yin canjaras uku a cikin rukuni a Euro 2016, wadda ta kai ga lashe kofin, amma ta kai zagayen gaba ne a matakin ƴar alfarma.









