Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United da Betis Arsenal da Sporting a Europa League
Manchester United za ta fafata da Real Betis a Europa League zagayen 'yan 16, yayin da Arsenal za ta fuskanci Sporting Lisbon.
Ranar Alhamis United ta doke Barcelona 2-1 a Old Trafford ta kai zagayen gaba da cin kwallo 4-3, bayan da suka yi 2-2 a Camp Nou a makon jiya.
Arsenal za ta karbi bakuncin wasa na biyu da kungiyar Portugal, bayan da Gunners ta yi ta farko a rukuninta.
Ita kuwa United za ta fara karbar bakuncin Real Betis a Old Trafford daga baya ta je Sifaniya.
Za a fara wasannin 'yan 16 a Europa League tsakanin 9 zuwa 16 ga watan Maris din 2023.
Arsenal ba ta buga wasannin cike gurbi ba, sakamakon ta daya da ta yi a rukunin farko, bayan cin wasa biyar daga shidan da ta yi.
Ita kuwa Sevilla mai Europa shida za ta kece raini da Fenerbahce, kungiyar Jose Mourinho, Roma za ta yi gumurzu da Real Sociedad - wadda ta yi ta daya a rukunin da ya hada da Manchester United.
An raba jadawalin ne tsakanin wadanda suka ja ragamar rukuni tun farko su takwas da wadanda suka kai bante, bayan karawar cike gurbi su takwas.
An kuma raba kungiyoyin ne ba tare da wata daga kasa daya ta hadu da 'yar uwarta ba.
Jawallin wasannin 'yan 16 a Europa League:
Union Berlin da Union Saint-Gilloise
Sevilla da Fenerbahce
Juventus da Freiburg
Bayer Leverkusen da Ferencvaros
Sporting Lisbon da Arsenal
Manchester United da Real Betis
Roma da Real Sociedad
Shakhtar Donetsk v Feyenoord