Abin da ya sa maza a Indiya suke gwada yadda raɗaɗin jinin al'ada yake

An wallafa

Jinin al'ada da irin mawuyacin halin da mata ke shiga idan suna yi - har yanzu wani abin ƙyama ne a galibin sassan Indiya.

Amma wani kamfe a Kerala, da ke Kudancin ƙasar na ƙoƙarin sauya hakan.

Masu shirya kamfe ɗin suna zuwa kantuna da kwalejoji a Gundumar Ernakulam su gwada yadda jinin al'ada yake domin maza su ɗanɗana zafin ciwon mara, a wani yunƙuri na fahimtar da mutane game da batun.

Wani bidiyo da kungiyar ta fitar a baya-bayan nan da ke nuna maza na ihu saboda zafin ciwo yayin da mata kuma ke kallo ya bai wa mutane dariya.

"Da zafi sosai. Ba zan so na sake ɗandana irin wannan ba," in ji Sharan Nair, wani mai faɗa a ji a kafafen sada zumunta da ya yi gwajin a wani kanti.

Gwajin wani ɓangare ne na wani shiri da aka yi wa taken "Cup of Life" a Turancin Ingilishi da zai riƙa rarraba kofunan yin al'ada tare da watsi da duk wasu labaran ƙarya da ake yaɗawa game da jinin al'ada.

Ɗan majalisa Hibi Eden daga Jam'iyyar Congress ne ya ƙaddamar da shirin hadin gwiwa da Ƙungiyar Likitoci a Indiya (IMA).

Lafiyar mata, musamman game da batutuwan da suka shafi jinin al'ada, abu ne da ba a cika tattaunawa a kai ba a India.

A yankuna da dama, ana kallon matan da suke jinin al'ada a matsayin waɗanda ba su da tsarki kuma ana mayar da su saniyar-ware a wuraren taron jama'a da kuma na ibada, har ma a madafi.

Yayin da aka samu sauyi a yankunan da ke birni, galibin mata har yanzu ba sa sakin jiki su yi magana game da jinin al'ada ko tsananin ciwon da suke fuskanta a lokacin da suke jinin al'ada.

Yayin da wasu kamfanoni a sassan duniya da kuma Indiya suka fara ba da hutun jinin al'ada, batun ya janyo ce-ce-ku-ce.

Amma masu shirya kamfe ɗin na fatan za su kawo sauyi a Kerala, ɗaya daga cikin jihohin da ake yi wa kallon sun samu ci gaba.

Lauya Sandra Sunny, wadda ta tsara shirin mai taken #ɗanɗanazafin, ta ce amfani da na'urar gwaji ce hanya mafi sauƙi ta jan ra'ayin mutane wajen tattaunawa da sauya tunani.

"Idan ka tambayi maza da ke makarantun gaba da sakandare abin da suka sani game da ciwon jinin al'ada, ba za su iya faɗa ba.

Amma idan ka tambaye su kamar - "Sun taɓa yin magana kan jinin al'ada da wani, me ya sa ba sa son yin magana a kai' - bayan amfani da na'urar gwajin, sun fi sakin jiki," in ji ta.

Na'urar na ɗauke da wayoyi biyu da ake ɗorawa a jikin mutum biyu a lokaci ɗaya sannan a danna maƙarin zafin daga ɗaya zuwa 10. Mista Nair ya tuna cewa ƴan matan da suka gwada "ba su ji komai ba" yayin da "mazan, har da ni, muke ta kururuwa".

Masu shirya shirin sun ce na'urar ta janyo tattaunawa a kwalejoji da ke gundunar Ernakulam.

Tawagar ɗalibai maza da ta gwada amfani da na'urar a wata kwaleji mai zaman kanta ta ce ba su iya daure wa zafin ba.

"Nan take suka buƙaci a kashe na'urar," kamar yadda Zeenath KS, ɗaya daga cikin ɗaliban da ke shirya shirin ya faɗa wa BBC.

Dr Akhil Manuel, Sakataren Ƙungiyar IMA kuma mai kula da kamfe ɗin Cup of LIfe, ya ce mata na nuna ko gezau ko da an kai yawan zafin zuwa maki tara amma da ƙyar maza ke kai wa mataki na huɗu.

Duk da cewa na'urar tana ba da kashi 10 cikin 100 na ainihin zafin jinin al'ada.

A watan Yuli ne wani kamfanin Amurka mai suna Somedays ya bai wa maza ƙwarin gwiwar yin amfani da na'urar gwajin zafin jinin al'ada domin su riƙa sanin irin halin da mata ke shiga.

Tuni miliyoyin mutane suka kalli bidiyon taron da aka wallafa a Tiktok. Mista Eden ya ce ya samu ƙwarin gwiwar yin kamfe ɗin ne bayan da ya soma wani shirin rarraba dubban kofunan jinin al'ada ga mata a wani ƙauye da ake kira Kumbalangi.

A farkon shekarar nan ne, gwamnan Kerala ya ayyana Kumbalangi a matsayin inda ake rarraba audugar jinin al'ada kyauta a Indiya.

An kammala Kamfe ɗin Cup of Life da aka soma shi watannin da suka gabata aka kuma tsara shirye-shirye da dama inda za a rarraba kounan jinin al'ada 100,000 domin kafa tarihi.

Amma Mista Eden ya ce babban maƙasudin shi ne ba da damar tattaunawa da kuma sauya fahimtar mutane game da jinin al'ada.

Dr Manuel ya ce galibin ƴan majalisa da ƙungiyoyi sun nuna sha'awarsu ga kamfe ɗin sannan sun tambayi yadda za su yi irinsa a yankunansu.

Sai dai ya ce akwai bukatar a yi aiki tare da al'umma, su fahimci yadda tsarin yake tare da samar da hanyoyin da za su taimaka muku wajen yin irin waɗan nan tattaunawa."