Hikayata 2023: Gwaraza uku da suka yi fice a gasar

Hikayata

Asalin hoton, hikayata

Bayanan hoto, Wannan ne karo na takwas na gasar Hikayata tun fara ta a 2016
An wallafa

Alkalan gasar rubutun kagaggun gajerun labarai ta mata zalla ta BBC Hausa, wato Hikayata sun zabi labarai guda uku da suka ciri tuta a gasar ta 2023.

Hakan na nufin alkalan sun fitar da guda ukun ne daga cikin 15 da suka yi fice.

Mata kusan 500 ne dai suka shiga wannan gasa, inda a matakin farko aka tantance labaran zuwa 400, kafin daga bisani a mataki na biyu na tantancewa wasu alkalai da ba ma'aikatan BBC ba ne suka zabi guda 30.

Wata tawagar alƙalan a mataki na karshe, bisa jagorancin ma'aikacin BBC sun zaɓi labaran 15 daga cikin 30 sannan kuma sun zabi gwarazan da labarinsu ya yi nasarar yin na ɗaya da na biyu da na uku.

Ga jerin labaran uku da suka yi fice:

  • Bakin Kishi - Aisha Abdullahi Yabo
  • Tuwon Kasa - Aisha Sani Abdullahi
  • Rina A Kaba - Aisha Adam Hussaini

Za a sanar da ta daya da ta biyu da ta uku a ranar Alhamis 30 ga watan Nuwamban 2023 yayin bikin karramawa a Abuja, babban birnin Najeriya.

Marubuta labaran da su ka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (nairan miliyan daya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu dari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu dari biyar) ga wadda ta zo ta uku.

Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai wadda ke samar da dama ga mata marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa.