Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Morocco ta ci Belgium ta hada maki hudu a wasa biyu
Morocco ta bai wa Belgium mamaki ta doke ta 2-0 a wasa na biyu a rukuni na shida a Gasar Cin Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.
A minti na 73 Morocco ta ci kwallon farko ta hannun Abdelhamid Sabiri, sannan Zakaria Aboukhlal ya kara na biyu daf da lokaci zai cika.
Mai tsaron ragar Belgium, Thibaut Coutois shi ne ya yi kuren kwallon farko a bugun tazara da Sabiri ya buga masa, saura minti 17 a tashi daga wasan.
A karawar Belgium wadda ba ta taba daukar kofin duniya ba ta je Qatar a matakin ta biyu a kan gaba a taka leda a duniyaq, biye da Brazil ta farko.
Filin wasa na Al Thumama ya rude da sowa da Morocco ta ci kwallo na biyu, wadda ta tashi 0-0 da Croatia ranar Laraba 23 ga Nuwamba.
Da wannan sakamakon Morocco ta hada maki hudu ta hau kan Belgium mai maki uku a rukuni na shida.
Croatia za ta fafata da Canada a daya wasan na rukuni na shida.