Wa zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Fifa na 2023?

An wallafa

Za a bayyana gwarzon ɗan ƙwallon kafa na duniya na Fifa na 2023 ranar Litinin 15 ga watan Janairu a Landan.

Cikin waɗanda ke takara a maza sun hada da Erling Haaland da Kylian Mbappe da kuma Lionel Messi.

Masu takara a fannin mata kuwa sun hada da Aitana Bonmati da Linda Caicedo da kuma Jennifer Hermoso .

Za a gabatar da bikin fitar da gwarzon ɗan kwallon kafa na duniya na Fifa a Landan, inda BBC za ta kawo muku yadda za a gudanar da taron daga 19:30 a bbc.com/sport

Masu yin zaben sun hada da wasu 'yan wasan tawaga ta kasa da kyaftin-kyaftin da kuma magoya baya da ke kada ƙuria a shafin Fifa.

Kowacce kasa a kan dauki kaso 25 cikin 100 daga ƙuri'unta wajen zabar fitatcen koci da kuma mai tsaron raga.

Akwai kuma ƙyautar Puskas, wani gwarzon dan kwallon kafar Hungary, mai suna Ferenc Puskas da ake bai wa wanda ya ci ƙwallo mafi ƙayatarwa.

Gwarzon bana da wanda zai karbi kyautar Puskas - za a auna kwazon da suka yi a fannin taka leda daga 19 ga watan Disambar 2022 zuwa 20 ga watan Agustan 2023.

Za kuma a auna ƙwazon mata daga 1 ga watan Agustan 2022 zuwa 20 ga watan Agustan 2023.

Akwai kuma ƙyautar wasa ba tare da gaba ba da ta mai goyon baya da ba kamarsa da fitattun ƴan wasa 11 na Fifa.

Masu takara a maza

Erling Haaland (Norway/Man City)

Kylian Mbappe (France/Paris St-Germain)

Lionel Messi (Argentina/Inter Miami)

Masu takara a mata

Aitana Bonmati (Spain/Barcelona)

Linda Caicedo (Colombia/Real Madrid)

Jenni Hermoso (Spain/Pachuca)