Man Utd na jiran Sancho ya yanke hukunci, Chelsea ta amsa tayin Nkunku daga Bayern

Sancho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United na shirin karɓan tayin Roma kan ɗaukan aron ɗan wasanta na Ingila Jadon Sancho, amma tana jiran ɗan wasan mai shekara 25 ya kammala shawararsa. (Fabrizio Romano)

Everton na duba zaɓin da suke da shi kan Tyler Dibling mai shekara 19, bayan rashin nasara a tayin da suka gabatar har sau uku - na karshen ya kai fam miliyan 37 - wanda Southampton ke fatali da shi. (Liverpool Echo)

Galatasaray ta gabatar da tayinta kan ɗan wasan Manchester City da Brazil, mai tsaron raga, Ederson mai shekara 31 kan fam miliyan 8.6. (Fabrizio Romano)

Chelsea na iya sayen ɗan wasan Argentina, Alejandro Garnacho mai shekara 21, daga Manchester United da mai buga tsakiya a Netherlands, Xavi Simons mai shekara 23, daga RB Leipzig idan sun shirya rabuwa da 'yan wasa biyu. (Sky Sports)

Arsenal da Manchester United da Napoli na zawarcin ɗan wasan tsakiya a Paris St-Germain da Koriya ta Kudu, Lee Kang-in mai shekara 24. (Caught Offside)

Roma ta amince da yarjejeniyar saye ɗan wasan Aston Villa da Jamaica, Leon Bailey mai shekara 28, kan zaman aron da aka yi wa kuɗi fam miliyan 1.7 da kuma zaɓin saye shi kan fam miliyan 20. (La Gazzetta dello Sport)

Nottingham Forest ta amince da yarjejeniya kan ɗan wasan Rennes mai shekara 23 daga Faransa, Arnaud Kalimuendo kan fam miliyan 25. (Telegraph)

Crystal Palace ta tuntuɓi Leicester City kan saye Bilal El Khannouss mai shekara 21, daga Moroko wanda ake son ya maye gurbin Eberechi Eze. (Athletic - subscription required)

Manchester United za ta sake farfaɗo da farautarta kan ɗan wasan tsakiya a Brighton da Kamaru, Carlos Baleba a kakar 2026. (Fabrizio Romano)

Chelsea ta shiga tattaunawa da Bayern Munich kan sayar da ɗan wasan Faransa, Christopher Nkunku mai shekara 27. (Mail)

Fenerbahce na shirin saye ɗan wasan Arsenal da Ukraine, Oleksandr Zinchenko mai shekara 28. (Sporx - in Turkish)