Ƴan Super Eagles da aka gayyata wasan Libya gida da waje

Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Augustine Eguavoen ya gayyaci ƙyaftin, William Ekong da Ademola Lookman da Moses Simon a wasan neman shiga gasar kofin Afirka da Super Eagles za ta kara da Libya.

Daga cikin sauran 20 da aka gayyata har da Olaoluwa Aina da Bruno Onyemaechi da kuma mai tsaron raga, Stanley Nwabali da Maduka Okoya.

Sauran sun haɗa da Oluwasemilogo Ajayi da Calvin Bassey da Wilfred Ndidi da Raphael Onyedika da Alex Iwobi da Taiwo Awoniyi da Victor Boniface da kuma Samuel Chukwueze.

To sai dai Victor Osimhen na jinya ba zai buga karawar ba da kuma Olsa Ndah mai taka leda a gasar tamaula ta Afirka ta Kudu.

Bright Osayi-Samuel ya samu goron gayyata, wanda bai yiwa Super Eagles wasa ba da Jamhuriyar Benin da Rwanda a watan Satumba.

Haka kuma an kira Kelechi Iheanacho da Fisayo Dele-Bashiru da Alhassan Yusuf Abdullahi da kuma Frank Onyeka.

Super Eagles za ta fafata da Libya ranar Juma'a a filin wasa na Godswill Akpabio a birnin Uyo a Akwa Ibom.

Daga nan tawagar Najeriya za ta Benin, domin sake karawa da Libya wato kilomita 19 tsakani daga Benghazi, inda za su fafata ranar Talata 15 ga watan Oktoba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƴan wasan da aka gayyata na Super Eagles:

Masu tsaron raga: Stanley Nwabali (Chippa United, South Africa); Maduka Okoye (Udinese FC, Italy); Amas Obasogie (Fasil Kenema SC, Ethiopia)

Masu tsare baya: William Ekong (Al-Kholood FC, Saudi Arabia); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce SK, Turkey); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal); Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Calvin Bassey (Fulham FC, England); Olaoluwa Aina (Nottingham Forest, England); Benjamin Tanimu (Crawley Town, England)

Masu wasan tsakiya: Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium); Alhassan Yusuf Abdullahi (New England Revolution, USA); Fisayo Dele-Bashiru (Lazio FC. Italy); Frank Onyeka (Augsburg FC, Germany); Alex Iwobi (Fulham FC, England)

Masu cin ƙwallaye: Samuel Chukwueze (AC Milan, Italy); Chidera Ejuke (Sevilla FC, Spain); Ademola Lookman (Atalanta FC, Italy); Kelechi Iheanacho (Sevilla FC, Spain); Victor Boniface (Bayer Leverkusen, Germany); Moses Simon (FC Nantes, France); Taiwo Awoniyi (Nottingham Forest, England)