Man City za ta je Champions League a baɗi - Marmoush

Asalin hoton, Getty Images
Omar Marmoush ya bugi kirji cewar Manchester City za ta koma kan ganiya, za kuma ta samu gurbin shiga Champions League a kaka mai zuwa.
Manchester City ta tashi 2-2 da Brighton a wasan Premier League karawar mako na 29 ranar Asabar a Etihad.
Marmoush ya ci wa City na biyu, bayan Pervis Estupinan na Brighton ya farke ƙwallon da Erling Haaland ya fara ci.
Daga baya ne City ta ci gida ta hannun mai tsare baya, Abdukodir Khusanov, hakan ya sa suka raba maki a tsakaninsu.
Marmoush ɗan wasan tawagar Masar, wanda ya koma City a Janairu kan £59m daga Eintracht Frankfurt ya ce ya kamata City take zuwa Champions League duk shekara.
Real Madrid ce ta yi waje da City a gasar zakarun Turai a wasan cike gurbin shiga gasar bana da aka sauya mata fasali.
City, mai rike da Premier League tana ta biyar a teburin Premier, Chelsea ce a mataki na huɗu.
City za ta je Bournemouth ranar Lahadi 30 ga watab Maris, domin buga FA Cup daga nan ta fafata da Leicester City a Premier League ranar Laraba 2 ga watan Afirilu.











