Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi karar Donald Trump da 'ya'yansa kan zambar biliyoyin dala
Babbar lauyar gwamnatin jihar New York a Amurka ta shigar da kara kan tsohon shugaban kasar Donlad Trump da manyan ‘ya’yansa uku, bisa zargin zamba.
Leticia James ta ce kamfanin tsohon shugaban, Trump Organisation da iyalan tsohon shugaban sun rika karyar kara darajar kadarorinsu, da biliyoyin dala don kawai su samu bashi mai gwabi-gwabi da suke so tare kuma da rage musu haraji.
Shi dai Trump ya yi watsi da zargin da cewa bita-da-kullin siyasa ne kawai.
A kan wannan kara da Atoni Janar din ta jihar New York ta shigar kan harkokin kasuwanci da iyalai da kuma tsohon shugaba Trump na wannan zamba da almundahana da ta ce sun yi ta kara gishiri da zuzuta darajar kasdarorin nasu,
wadanda ta ce darajarsu ba ta kai yadda suka ayyana ba, tana neman kotu ta umarci wadanda ta shigar da karar a kansu da su biya tara ta dala miliyan 250.
Bayan haka kuma tana neman kotu da ta haramta wa Trump din da iyalansa gudanar da harkokin kasuwanci a New York.
Shari’ar wadda tsohon shugaban ya bayyana ta da kutungwilar siyasa, ta yi masa bi-ta-da-kulli ta hada da manyan 'ya’yansa wato Donald Jr da Ivanka da Eric Trump tare da wasu manyan jami’ai na kamfaninsa, Trump Organisation, Allen Weisselberg and Jeffrey McConney.
Babbar lauyar ta jihar New York da ta gabatar da karar ta ce ta yi hakan ne bayan bincike na tsawon shekara uku.
A wata sanarwa ta ce da taimakon ‘ya’yansa da manyan jami’an kamfaninsa Donald Trump ya yi karyar zuzuta dukiyarsa da biliyoyin dala domin azurta kansa ta hanyar da ba ta dace ba da kuma zambatar dukiyar al’umma.
Ta ce gidan shi kansa Mista Trump wanda yake dogon benen nan nasa Trump Tower, da aka yi masa kudi Dala miliyan 327 na daga cikin kadadrorin da ake zargin kara gishiri a darajarsu.
Ta kara da cewa: "Babu wani gida irin wannan a birnin New York da aka taba sayarwa a kusa da wannan kudi ma.’’ In ji ta.
Ms James na bukatar kotu ta hana tsohon shugaban da ‘ya’yansa aiki a matsayin jami’ai ko daraktoci a duk wata harkar kasuwanci a New York.
Haka kuma tana son a haramta wa kamfanin na Trump shiga duk wat hada-hada ta ta gidaje a can tsawon shekara biyar.
Babbar lauyar ta gwamnatin New York, wadda ‘yar jam’iyyar Democrat ce da kuma take neman sake tsayawa takara a lokacin zaben rabin wa’adi na majalisar dokokin Amurkar a watan Nuwamba ta fitar da wannan sanarwa ne bayan da a baya ta yi watsi da tayin sasantawa a daya daga cikin bincike-bincke da aka dade ana yi a kan harkokin kasuwancin kamfanin na Trump.
Da yake suka ga zargin a shafinsa na intanet, Truth Social, Mista Trump ya bayyana Ms James, wadda bakar fata ce a matsayin mai nuna wariyar jinsi.
Wadda ya ce, ta kasa cimma burinta na zama gwamna, bayan da kasa samun goyon bayan jama’a, ta karkata ga bi-ta-da-kullin siyasa.
Ko a baya ma Mista Trump ya zargi Ms James da neman ramuwar gayya ta siyasa, inda ya bayar da misalain kalaman da ta yi kafin a zabe ta a mtsayin babbar lauyar a
2018, inda a kalaman ta lashi takobin gurfanar da shi gaban shari’a tare da ayyana shi a matsayin shugaban kasar da ba halartacce ba.
Duk da cewa Mista Trump ba ya cikin ‘yan takara a zaben na rabin wa’adi na Nuwamba, ya ci gaba da kasance dan siyasar Republican da aka fi jin amonsa a jam’iyyar, wanda kuma ake jita-jitar yana da nufin sake neman takarar shugaban kasar a 2024.
Wannan dai daya ce daga cikin jerin shari'u daban-daban da tsohon shugaban na Amurka, Donald Trump ke fuskanta.
Shari'un da suka hada da na zargin almundahana da na batun takardun sirri na gwamnati da kuma kokarin sauya sakamakon zaben shugaban kasa na 2020.
Trump ya musanta aikata ba daidai ba a dukkanin tuhume-tuhumen.