Abu biyar da ya kamata ku sani kan wasan Atletico da Barca a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Hansi Flick ya ja kunnen ƴan Barcelona da su kula kada su kara sakaci a wasan da za su fafata a gidan Atletico a La Liga ranar Lahadi, kamar yadda suka yi a baya.
Barcelona ce ta biyu a teburin la Liga, yayin da Atletico ce ta uku da Real mai jan ragama, wadda ta yi nasara 2-1 a gidan Villareal ranar Asabar.
A karawar La Liga da suka yi a cikin Disamba, Barcelona na cin 1-0 daga baya Atletico ta farke ta hannun De Paul daga baya Alexander Sorloth ya ci na biyu.
Haka a Copa del Rey cikin Fabrairu, Atletico ta fara zura biyu a raga daga baya Barcelona ta farke ta kara biyu, amma kan tashi Atletico ta farke aka tashi 4-4.
A makon jiya Real ta yi waje da Atletico a Champions League, ita kuwa Barcelona ta kai kwata fainal, sakamakon doke Benfica gida da waje.
Wasu baturuwa biyar kan wasan Atletico da Barca
Burin Atletico
Ƙungiyar da Diego Simeone ke jan ragama ta samu maki uku a wasan farko a bana a gidan Barcelona.
Kafin nan ta je Barcelona wasa 17 ba tare da yin nasara ba, sai a wannan kakar, kuma Atletico na fatan yi wa Barcelona gida da waje a La Liga tun bayan 2005/2006.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cin wasa ba tare da an zura ƙwallo ba a raga
Wasa huɗu baya tsakanin Atletico da Barcelona a Metropolitano, kowacce ta yi nasarar cin wasa biyu.
Kuma duk wadda ta yi nasara ba a zura mata ƙwallo a raga a wasan na hamayya.
A kakar 2020/21 lokacin korona Atletico ta yi nasara 1-0 a kakar gaba kuma ta ci 2-0.
Daga baya batun ya canja inda Barcelona ta je ta ci 1-0 a 2022/23, sannan a kakar gaba ta kara nasara amma da cin 3-0 a Madrid.
Kenan Atletico za ta yi fatan kada a doke ta karo na uku a jere a gida ba tare da cin ƙwallo ba a karo na biyu a gida a tarihin fafatawa a tsakaninsu.
Birnin Madrid farin cikin Barcelona
A baya birnin Madrid kan bai wa Barcelona wahalar samun maki, yanzu abin ya sauya, inda Barcelona ta haɗa maki a wasa uku a birnin a kan Rayo Vallecano da Real Madrid da canjaras a Getafe.
Idan Barcelona ta ci wasan ranar Lahadi zai zama karo na huɗu da cin karawa a Madrid, balle idan ba a zura mata ƙwallo ba a raga, za ta maimaita bajintar koci, Ernesto Valverde a 2019.
Gavi kan taka rawar gani a wasa da Atlético
Gavi ɗan wasan Barcelona yana da tarihi a kan Atletico, wanda a wasa biyar baya ya ci ƙwallo ya bayar da biyu aka zura a raga, irin ƙwazon da ya yi a wasa da Elche.
Atletico ta yi wasa 14 ba tare da rashin nasara ba
Kawo yanzu Atletico ta yi karawa 14 a jere ba tare da rashin nasara ba a La Liga.
Wasan da aka yi nasara a kan Atletico a Metropolitano, shi ne a fafatawa da Osasuna da ta ci 4-1 wasa na biyu daga shi sai na karshe a bara.
Shin ko Barcelona za ta takawa Atletico Burki.










