Martinelli ya bukaci Arsenal ta ɗauki darasi a wasan Aston Villa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Gabriel Martinelli ya ce ya kamata Arsenal ta ɗauki darasi kan abinda ya faru a wasan da ta ci karo da koma baya da Aston Villa ranar Asabar a Emirates.

Gunners ta ci karo da koma baya a gida a Premier League, wadda ta tashi 2-2 da ƙungiyar Villa Park,

Hakan ya sa tazarar maki tsakaninta da Liverpool ta ɗaya ya koma shida da ƙwantan wasa da za ta yi nan gaba da Everton.

Martinelli ne ya fara ci wa Gunners ƙwallo tun kan hutu, sannan Kai Havertz ya kara na biyu da suka shiga zagaye na biyu a wasan na hamayya.

Daga baya ne Villa ta kara sa ƙwazo da ta kai ga zare ƙwallayen ta hannun Youri Tielemans da Ollie Watkins cikin minti takwas tsakanin na farko da na biyu.

Ranar Laraba Arsenal za ta buga Champions League da Dinamo Zagreb a Emirates daga nan ta fuskanci Wolverhampton a Premier League.

William Saliba bai buga wasan ba, kuma Mikel Arteta ya sanar cewar sun damu da rashin mai tsaron baya, mai jinya.

Haka kuma ana ci gaba da auna koshin lafiyar Saliba, kenan nan gaba Arsenal za ta yi karin bayani kan koshin lafiyar ɗan wasan.

Ƴan ƙwallon Arsenal da ke jinya sun haɗa da Bukayo Saka da Gabriel Jesus da Ethan Nwaneri da Riccardo Calafiori da Ben White da kuma Takehiro Tomiyasu.