Tim Walz: Tsohon malamin makaranta da zai yi wa Kamala Harris mataimaki a zaɓen shugaban Amurka

- Marubuci, Sam Cabral
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Mai yi wa jam'iyyar Democrat takarar shugaban ƙasa, Kamala Harris, ta zaɓi Mista Tim Walz a matsayin wanda zai yi mata mataimaki a zaɓen shugaban ƙasar ta Amurka da ke tafe.
Tim mai shekara 60, mutum ne da aka bayyana da mai salon magana da kuma ya kasance mai sukar jam'iyyar Republican.
Ya taɓa zama malami, kocin kwallon kafa da kuma jami'in tsaro na ƙasa, kafin ya shiga harkar siyasa.
Ya taɓa wakiltar jam'iyyarsa ta Democrat a matakin gunduma, inda daga bisani ya zartar da tsare-tsaren masu ra'ayin rikau a matsayinsa na gwamnan jihar Minnesota.
Walz wanda ya fito daga jihar Nebraska, ya kasance manomi da kuma yin farauta lokacin damina, inda bayan nan kuma ya samu gurbi a cikin rundunar sojojin ko-ta-kwana ta Amurka yana shekara 17. Ya yi aikin sa-kai a rundunar har na tsawon shekara 24.
Mahaifinsa, wanda malamin makaranta ne, shi ya ba shi kwarin gwiwar cewa ya shiga rundunar sojin kafin cutar daji ko kuma kansa ta kashe shi, lokacin ɗansa Mista Walz yana da shekara 19.
Gwamnan na jihar Minnesota ya kuma bayyana yadda wasu asusun kyautata walwalar jama'a na gwamnati ya taimaka wa mahaifiyarsa, kuma gidauniyar GI Bill ce ta biya masa kuɗin karatu.
Walz wanda ya samu horo a fannin koyarwa, ya shiga aikin malanta na shekara ɗaya a China a lokacin da aka yi kiyasin kiyashi a birnin Tiananmen.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga baya ya yi zaman hutu da amaryarsa Gwen Whipple kuma ya shirya ziyarce-ziyarce na taruka kan ilmi zuwa China ga ɗaliban Amurka.
Bayan dawowa gida Nebraska, Mista Walz ya zama malami da kuma kocin kwallon kafa har zuwa lokacin da matarsa - wadda ita malama ce a wata makaranta - ta janyo shi komawa zuwa mahaifarta Minnesota. Yanzu suna da yara biyu.
A matsayinsa na koci a makarantar Mankato, Mista Walz ya taimaka wajen kafa wani shirin kwallon kafa da ya janyo makarantar ta samu damar lashe kofi na farko.
Ya kuma samu yabo bayan da ya amince ya zama mai ba da shawara a makarantar a ɓangaren masu auren jinsi a lokacin da ake yin Allah-wadai da batun.
Ana kallon shigarsa harkar siyasa a matsayin abin bazata.
A 2004, ya mara wa wasu ɗalibansa biyu baya zuwa wajen kamfe ɗin George W Bush, sai dai ɗaliban - ƴan Democrat sanye da alamomin John Kerry - an bayyana su a matsayin barazana ga shugaban ƙasar, inda aka buƙaci su bar wajen.
Bayan fusata da lamarin, Mista Walz ya yarda ya shiga kamfe ɗin takarar shugaban ƙasa na John Kerry, wani abu da ya sa ya fara zama sananne har ta kai ya shiga zaɓe a 2006.
Ya fafata a yanki da ya kasance yawanci manoma waɗanda ke rayuwa a faɗin Minnesota, waɗanda kauyawa ne masu goyon bayan Republican.
Sai dai Mista Walz ya yi kamfe a matsayin mutum mai son kula da ma'aikata, abin da ya janyo aka samu bazata, inda aka kayar da ɗan takarar Republican a wancan lokaci. Daga baya Walz ya samu nasara a lardin har sau biyar.

Asalin hoton, Getty Images
A tsawon shekara 12 da ya shafe a majalisa, abu ne mai wuya a gano akidojinsa.
Ya amince da kuri'ar da aka yi ta kara mafi kankantar albashi a majalisar dokokin ƙasar, da kuma buƙatar rage gurɓatacciyar iska da kamfanoni ke fitarwa.
Har wa yau, ya kaɗa kuri'a domin Amurka ta ci gaba da bayar da kuɗi a yake-yaken Iraƙi da Afghanistan, da kuma tsaurara tsaro don hana bakin haure shiga ƙasar, har ma da hana ƙoƙarin da gwamnatin Obama ta yi na ceto bankuna daga matsalar da suka shiga, da kuma kamfanonin ƙera motoci bayan matsalar kuɗi da aka fuskanta a 2008.
Mista Walz ya lashe zaɓen gwamnan jihar Minnesota a 2018 da sama da kuri'u 11, sai dai wa'adinsa na farko ya gamu da iftila'in annobar korona da kuma kisan George Floyd da wani ɗan sanda ya yi a Minneapolis.
Ƴan Republican sun soki Mista Walz saboda rashin aika dakarun ko-ta-kwana duk da cewa zanga-zangar adawa da kisan da aka yi a lokacin ta rikiɗe zuwa tarzoma.
Sai dai an sake zaɓar gwamnan karo na biyu, inda nan kuma mulkinsa ya ga yanda Democrat ta samu kuri'a ɗaya a majalisar jihar.
Jam'iyyar Democrat ta amince da ƴancin zubar da ciki, kaɗa kuri'a kan biyan iyalai da kuma kuɗin da ake bai wa marasa lafiya, tsaurara dokokin mallakar bindiga, halasta noman tabar wiwi, samar da abinci kyauta a makarantu da kuma saukaka mallakar gidaje.
Duk da cewa Mista Walz ba sananne bane sosai a faɗin ƙasar, amma an yi ta magana a kansa a baya-bayan nan saboda yadda yake kwatanta ƴan Republican.
"Mutane ne da ke abubuwan mamaki," kamar yadda ya faɗa, abu kuma da aka yayata shi. "Suna son su haramta takardu. Suna son kasancewa cikin ɗakin likitanku."
Sai dai tuni ƴan Republican suka fito suka soki irin salon mulki da ya yi a Minnesota.
Tom Emmer, mutum na uku mafi girma a Republican a majalisar wakilan Amurka, ya zargi Mista Walz da ƙoƙarin mayar da jihar Minneosta zuwa ta Ms Kamala Harris kamar jihar mahaifarta California.
Sai dai ƙawayensa, ciki har da shugabannin jam'iyya, na ganin Mista Walz na da kwarewa wajen janyo ra'ayin mazu zaɓe a birane da kauyuka.
Angie Craig, ƴar jam'iyyar Democrat a majalisar wakilan Amurka da ke son sake tsayawa takara, ta yaba wa Mista Walz da cewa shi jagora ne na gari.
Ta faɗa wa BBC cewa tana da yakinin cewa Mista Walz zai kasance mutum da ya fi ya zo taimaka a takarar Harris, a matsayinsa na mai nasara wanda bai taɓa shan kaye a zaɓuka masu zafi da aka fafata ba.











