'Yan Liverpool 12 ne za su buga wa tawagoginsu wasa

Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

'Yan wasan Liverpool 12 ne aka gayyata tawagoginsu, domin buga wasanni a makon nan da na gobe.

A cikin makon nan za a buga wasannin neman shiga gasar kofin nahiyar Turai, Euro 2024 da ta Afirka da wasannin sada zumunta.

'Yan wasan Liverpool da aka gayyata sun hada da Virgil van Dijk da Cody Gakpo da Ibrahima Konate da Andy Robertson da kyaftin Jordan Henderson.

Sauran sun hada da Diogo Jota da Kostas Tsimikas da Caoimhin Kelleher da Mohamed Salah da Naby Keita da Harvey Elliott da kuma Curtis Jones.

Kyaftin, Jordan Henderson, yana cikin 'yan wasan da Ingila ta gayyata buga wasan neman shiga Euro 2024.

Ingila za ta fara da ziyartar Italiya ranar 24 ga watan Maris, kwana uku tsakani ta karbi bakuncin Ukraine a Wembley.

Virgil van Dijk da Cody Gakpo za su kece raini da Faransa ranar 24 ga watan Maris da fuskantar Netherlands kwana uku tsakani.

Haka kuma tawagar Faransa, mai Ibrahim Konate za ta fuskanci Jamhuriyar Ireland, mai dan wasan Caoimhin Kelleher’.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kyaftin din Scotland, Andy Robertson zai buga wa kasar wasan da za ta yi da Cyprus ranar 25 ga watan Maris da kuma Sifaniya kwana uku tsakani.

Portugal mai Diogo Jota za ta kece raini da Liechtenstein ranar 23 ga watan Maris, sannan kwana uku tsakani ta fuskanci Luxembourg.

Shi kuwa Kostas Tsimikas zai buga wa tawagar Girka wasan da za ta yi da Gibraltar ranar 24 ga watan Maris da kuma Lithuania kwana uku tsakani.

Shi kuwa Mohammed Salah zai yi Masar karawar gida da waje da Malawi a wasan neman shiga gasar kofin Afirka.

Za su fara karawa ranar 24 ga watan Maris, sannan wasa na biyu kwana hudu tsakani.

Haka kuma Naby Keita zai yi wa Guinea wasan da za ta kara da Habasha ranar 24 ga watan Maris a karawa ta biyu kwana uku tsakani.

Su kuwa matasan Liverpool 'yan kasa da shekara 21, Harvey Elliott da Curtis za su buga wa Ingila wasan sada zumunta da Faransa ranar 25 ga watan Maris da Croatia kwana uku tsakani.

Darwin Nunez ba zai buga wa Uruguay wasa ba, sakamakon jinya da yake yi.