Leicester ta yi watsi da tayin Chelsea kan Fofana, Barca za ta sayar da Aubameyang

Fofana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fofana
An wallafa

Leicester City ta yi watsi da tayin da Chelsea ta yi mata na kudi £60m domin daukar dan wasan kungiyar, dan asalin Faransa, Wesley Fofana mai shekara 21. (Mail)

Yanzu haka Chelsea na kokarin ganin ta kara kudin tayin zuwa £70m domin ganin ko Leicester din za ta sallama. (Times - subscription required)

Barcelona na da niyyar sayar da dan wasanta na gaba, dan asalin kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 33 ga Chelsea. (Mirror)

Nottingham Forest ta fara tattaunawa da Southampton domin dauko Che Adams, dan asalin kasar Scotland, mai shekara 26. (Football Insider)

Har wa yau Forest din ta nuna sha’awar dauko dan wasan tsakiya na Wolves, mai shekara 22, Morgan Gibbs-White, dan asalin kasar Ingila. (Sky Sports)

Tottenham na gab da kammala dauko dan wasan baya na Udinese, mai shekara 19, Destiny Udogie kan kudi £21m. (Telegraph)

Dan wasan Burnley, Maxwel Cornet, mai shekara 25, zai fuskanci gwajin lafiya a West Ham bayan da ta amince da biyan diyyar sayen dan wasan, £17.5m, kan dan wasan, dan asalin kasar Ivory Coast. (Mail)

Manchester United za ta janye daga ja-in-jar da take yi da Chelsea kan dauko dan wasan tsakiya na Barcelona, dan asalin kasar Netherlands, Frenkie de Jong, mai shekara 25. (Mirror)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

 

Lucas Torreira ya amince ya tafi Galatasaray, wadda za ta biya Arsenal kudi tsakanin £5m da £6m domin daukar dan wasan na tsakiya dan asalin kasar Uruguay, mai shekara 26. (Fabrizio Romano)

Juventus na son ganin ta sayi dan wasan gaba na Netherlands, Memphis Depay, mai shekara 28, daga Barcelona. (Sport - in Spanish)

Real Madrid na sa ran Nice za ta rage kudin da ta sanya har yuro miliyan 40 (£33.7m) ga duk mai son daukar Amine Gouiri, domin ganin ta sayi dan wasan na gaba, dan asalin kasar Faransa, wanda ke da shekara  22. (Sport - in Spanish)

Sabon mai horas da ‘yan wasan Paris St-Germain, Christophe Galtier na sa ran dauko karin ‘yan wasa uku, bayan nasarar dauko Renato Sanches, mai shekara 24, dan asalin kasar Portugal  daga Lille, wanda shi ne na hudu da kungiyar ta sayo cikin kwanakin nan. (Sport - in Spanish)

Dan wasan baya, dan asalin kasar Sifaniya Angelino na gab da tafiya Hoffenheim a matsayin aro daga RB Leipzig, duk kuwa da cewa kungiyoyi irin su Brighton, da Barcelona da kuma Sevilla sun nuna sha’awar daukar dan wasan mai shekara 25. (AS - in Spanish)