Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United na fuskantar turjiya kan Dorgu, babu tabbas kan makomar van Dijk
Lecce na "ƙoƙarin yin turjiya" kan yunƙurin Manchester United na ɗaukar Patrick Dorgu, Neymar a shirye yake ya sadaukar da wani ɓangare na albashinsa don komawa Santos, Aston Villa na sha'awar ɗan wasan bayan Chelsea Axel Disasi.
Shugaban Lecce Sticchi Damiani ya ce kulob ɗin yana "ƙoƙarin bijire wa" matsin lambar da Manchester United ke yi na sayen ɗan wasan bayan Denmark Patrick Dorgu, mai shekara 20, wanda kulob ɗin Italiya ya ƙimanta a kan Yuro miliyan 40 (£33.8m). (Football Italy)
Ɗan wasan gaban Brazil Neymar, mai shekara 32, a shirye yake ya bar wani kaso mai yawa na albashinsa don barin Al-Hilal ya koma tsohon kulob ɗinsa na Santos da ke ƙasarsa. (Footmercato)
Ɗan wasan tsakiya na Argentina Emiliano Buendia, mai shekara 28, ya amince da tsawaita kwantiragin shekara ɗaya da Aston Villa, yayin da ƙungiyoyi a Jamus da Italiya da kuma Saudiyya ke zawarcinsa. (Athletic)
Aston Villa na tattaunawa da ɗan wasan bayan Argentina Juan Foyth, mai shekara 27, daga Villarreal bayan da ta kasa ɗauko ɗan wasan bayan Faransa Loic Bade, mai shekara 24, daga Sevilla. (Talksport)
Aston Villa na zawarcin ɗan wasan baya na Chelsea ɗan ƙasar Faransa Axel Disasi, mai shekara 26, yayin da suke ƙoƙarin kawo mai tsaron baya kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan wasa ta hunturu. (Football Insiders)
Kyaftin ɗin Liverpool Virgil van Dijk ya ce bai san "abin da zai faru nan gaba ba", yayin da kwantaraginsa ke shirin ƙarewa a bazara. (Liverpool Echo)
Ɗan wasan baya na Brentford Mads Roerslev, mai shekara 25, zai tashi zuwa Wolfsburg ranar Litinin don kammala gwajin lafiyarsa bayan da ƙungiyoyin biyu suka cimma yarjejeniyar aro ta tsawon wata shida ga ɗan wasan bayan na Denmark, tare da zaɓin siya. (Sky Sports Germany)
AC Milan za ta miƙa tayin kusan €33-34m kan ɗan wasan Mexico Santiago Gimenez, duk da cewa Feyenoord na son €40m kan ɗan wasan mai shekaru 23. (Calciomercato)
Ɗan wasan Leicester City da Bangladesh Hamza Choudhury, mai shekara 27, na shirin komawa Sheffield United a matsayin aro a yarjejeniyar da ta haɗa da zaɓin siya. (Athletic)