Abin da ya sa Biden ba ya so Isra'ila ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran hari

Asalin hoton, Israeli Prime Minister's Office
- Marubuci, Jeremy Bowen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban ƙasar Amurka da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun yi tattaunar wayar tarho ta minti 30 da aka daɗe ana jira - wadda ake tunanin ita ce tattaunawarsu ta farko tun watan Agusta.
Sun yi tattaunawa game da batun yunƙurin Isra'ila na mayar da martani kan hare-haren da Iran ta kai mata.
Fadar shugaban ƙasar Amurka ta bayyana wayar a matsayin "kai-tsaye" kuma "mai amfani" sannan ta ce Biden da Netanyahu sun amince su cigaba da "tattaunawa" a kwanaki masu zuwa. Ita ma mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Haris ta shiga ganawar wayar.
Da yake magana bayan ganawar, ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant ya ce hare-haren da za su kai Iran za su "munana, kuma za su bayar da mamaki."
Abubuwa biyu ne suka sa aka damu da tattaunawar tasu. Na ɗaya shi ne yadda Biden yake jan ƙafa da kuma ƙokarin tsame Amurka daga shiga yaƙi da Iran, wanda yake tunanin bai da amfani kuma yake da hatsari.
Ɗayan kuma shi ne wasu ƴan Isra'ila suna ganin wannan wata dama ce da Isra'ila ta gasa wa Iran - babbar maƙiyarrta a duniya - aya a hannu.
Isra'ila tana ganin ta samu nasara a Lebanon, kuma tana kan samu, ba kamar yaƙin da take yi a Gaza ba.
Duk da hare-haren Isra'ila ke yi a Gaza, wanda ya ci mutum kusan 42,000, waɗanda mafi yawansu fararen hula ne, har yanzu Benjamin Netanyahu yana ganin bai samu nasarori biyu da yake buƙata ba - ganin bayan Hamas da ceto waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su.
Har yanzu Hamas na cigaba da yaƙin, kuma tana cigaba da riƙe da kusan ƴan Isra'ila 100 da ta yi garkuwa da su, waɗanda ake tunanin mafi yawansu ma sun rasu.
Irin nasarar da Isra'ila ta samu a kan Hezbollah ta Lebanon da Hamas a Gaza ne ya sa wasu ƴan ƙasar suke so ta ƙaddamar da yaƙi a Iran.
A tunaninsu, ƙasar za ta samu nasara idan ta kai hare-hare a Iran ta sama.
Ɗaya daga cikin wuraren da mutanen Isra'ila suke so a kai hare-hare su ne wasu tsaunukan da a ciki akwai wuraren haɗa makamashin nukiliya na Iran, waɗanda Isra'ila da wasu ƙasashe suke fargabar ana haɗa bama-bamai.

Asalin hoton, EPA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaba Biden ya bayyana a fili cewa ba ya goyon bayan kai hari a kan makamashin nukiliya na Iran.
Amurka ta yi amannar cewa Iran ba ta shirya haɗa makamashin nukiliya ba a nan kusa. Amma ƙaddamar da hare-hare a kanta zai iya tursasa ta ta fara haɗa makamin.
Ɗaya daga cikin na gaba-gaba wajen ingiza Netanyahu ya yi watsi da kashedin Amurka na hana kai wa Iran hari, shi ne tsohon firaiministan Isra'ila Naftali Bennett, wanda ya ce bai kamata Isra'ila ta yi wasa da damar da ta samu na illata Iran ba.
Kamar yadda irin fahimtar ɗan siyasar hamayya kuma tsohon janar, Benny Gantz, shi ma Bennett ya yi amannar cewa yanzu an riga an raunana Iran, ba ta ƙarfi kamar yadda take a gomman shekaru da suka gabata saboda irin illar da aka yi wa Hezbollah da Hamas.
"Iran tana amfani da Hezbollah da Hamas ne a matsayin garkuwanta. Su ne suke ba ta kariya da ƙarfin gwiwa," in ji Bennett.
"Amma yanzu duka ƙungiyoyin biyu an karya lagonsu."
Bennett ya ce yanzu wata dama ce da ya kamata Isra'ila ta yi amfani da shi wajen illata Iran.
"Idan Iran ta samu damar mallakar nukiliya, za ta iya amfani da ita domin kare martabar mulkinta. Wannan na nufin za ta yi amfani da makamin wajen rugurguza Gabas ta Tsakiya."
Bennett ya yi waiwaye a kan wasu hare-haren Isra'ila guda biyu a kan wuraren haɗa makamashin nukiliya da Isra'ila ta yi a baya, wanda a cewarsa su ne suka taimaka wajen samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya - a Iraqi a 1981 da Syriya a 2007.
"Mutane ba su so ba," in ji Bennett. "Amma mun ceci duniyar daga (Bashar al-) Assad.
"Aiki ne a gabanmu na hana makamashin nukiliya shiga ɗaya daga ɗaya cikin gwamnati mafi muni a duniya. Kowa na kushe mu a kan wannan yunƙuri, amma aiki ne mai kyau muke yi.

Asalin hoton, Oren Rosenfeld
Tun watan Afrilu Iran da Isra'ila suke musayar yawu, bayan Isra'ila ta kashe wani babban janar na sojin Iran a ofishin jakadancin Iran da ke Syria.
Iran ta mayar da martani da wasu hare-hare a Isra'ila. Kuma tun lokacin ake ta zaman tankiya.
A ranar Talatar da ta gabata ce aka sake sabunta takun-saƙar, bayan Iran ta ƙaddamar da wasu hare-hare a Isra'ila a matsayin martanin hare-hare a kan Hezbollah a Lebanon da kashe jagoranta ƙungiyar Hassan Nasrallah.
Bayan hare-haren makamai masu linzamin na Iran a Isra'ila ne firaiministan Isra'ila ya ce zai mayar da martani.
Shugaba Biden bai damu ba wajen hana hare-haren Isra'ila a Gaza. Sannan ya yi "kira" da Isra'ila da ta sauƙaƙa wa fararen hula a Lebanon. Amma ya dage kai ta fata cewa lallai kada Iran ta kai hari a kan makamashin nukiliyar Iran.
Shugaba Biden ya ce dole Isra'ila ta kare kanta - amma ba sai ta kai hari a kan makamashin nukiliyar Iran ba- ko kuma matatar manta.
Amurka na fargabar kada a shigar da ita yaƙin da ba ta shirya ba. Sannan akwai fargabar idan aka kai wa Iran hare-hare, za ta ita yanke shawarar fara haɗa nukiliya.
Yanzu abun jira a nan gaba shi ne irin martanin da Isra'ila za ta mayar - wanda zai iya zuwa a kowane lokaci daga yanzu.










